1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages
Wrong language? Change it here. DW.DE has chosen Hausa as your language setting.
  • Karikatur von den südafrikanischen Künstlern John Swanepoel und John Curtis (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Matsayi na daya ga zanen kungiyar AU da bata da kafafun tafiya

    Zanen mai suna "Shin mun iso ne?" ya fito daga masana zane-zane na Afirka Ta Kudu John Swanepoel da John Curtis, wadanda a mahaifarsu ake kiransu "Dr Jack & Curtis". Su suka zama na daya a takarar wannan shekara ta zane-zane da kungiyar nan mai suna "3.World Journalists Network" ta nan Jamus ta shirya. Taken gasar ta duniya baki daya a bana shine: Shekaru 50 na hada kan Afirka.

  • Karikatur von Victor Ndula aus Kenia (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Jirgin ruwa yazo a matsayi na biyu

    "Hadin kai abune da ya zama a'ala idan Afirka tana son ci gaba da wanzuwa" - Wannan dai shine taken da Victor Ndula daga Kenya ya baiwa zanensa. Hakan ya bashi damar kasancewa na biyu a gasar ta zane-zane.

  • Karikatur von Samuel Mwamkinga aus Tansania (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Matsayi na uku: Ja ni-in-ja ka

    Samuel Mwankinga daga Tanzaniya shine ya dauki matsayi na uku. Ta hanyar zane ya nunar da "Kalubalen dake gaban kungiyar hada kan Afirka".

  • Karikatur von Ssentongo Jimmy Spire aus Uganda (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Kare mai haushi baya cizo

    Wasu daga cikin wadanda suka shiga gasar ta zane-zane, sun maida hankalinsu ga rawar da Afirka take takawa a al'amuran siyasar duniya. Kamar dai wannan zanen mai suna "Magana da murya daya" daga Ssentongo Jimmy Spire na kasar Uganda

  • Karikatur von Junior Heritier Bilaka aus der Demokratischen Republik Kongo (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Gagarumin nauyi

    Shima Junior Heritier Bilaka daga Jamhuriyar Demokradiyar Kongo ya gabatar da zanen da ya nuna angizon da manyan daulolin duniya suke dashi kan yan siyasar Afirka

  • Karikatur von Tayo Fatunla aus Nigeria (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Tafiyar Hawainiya

    Tayo Fatunia daga Najeriya a zanensa, ya nuna cewar bai ga wani abu mai haske a daidai lokacin da Kungiyar Hada Kan Afirka take bikin cika shekaru 50 ba.

  • Karikatur von Dick Esale, Demokratische Republik Kongo (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Afirka tana cin wuta

    Wannan zane dake nuna Afirka tana cin wuta, ya fito ne daga gwanintar Dick Esale na Jamhuriyar Demokradiyar Kongo

  • Karikatur von Guelajo Silá, Guinéa Bissau (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Hangen makoma mai haske

    Daya daga cikin zane-zane yan kalilan dake nuna haske ga Afirka ya samu ne daga Guelajo Sile na Guinea Bissau. A ganinsa, shekara ta 2013 "shekara ce ta Afirka", wanda ma hakan shine taken zanen da yayi.

  • Karikatur von Haswel Kunyenje, Malawi (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    A tuna baya, a sabunta gaba

    Wannan shine yadda Haswel Kunyunje daga Malawi ya hangi canza sunan Kungiyar Hada Kan Kasashen Afrika(OAU zuwa Kungiyar Hada Kan Afrika(AU) a shekara ta 2002.

  • Karikatur von Michaël Maloji M., Demokratische Repubik Kongo
(Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Afirka nahiyar Ka zo-Na zo

    Mai zane-zane Michael Maloji M. daga Jamhuriyar Demokradiyar Kongo ya nuna irin hangensa ga Kungiyar Hada Kan Afirka.

  • Karikatur von Siphiwo Sobopha S. Sobopha, Südafrika (Foto: DWJN)

    Kungiyar Hada Kan Afirka ta hanyar zane

    Jigon kungiyar AU

    "Kafafun da Afrika ta tsaya kansu" shine sunan zanen hoton da Siphiwo Sobopha daga Afirka Ta Kudu ya shiga gasar ta zane-zane dashi. Wadanda suka shirya gasar sun nuna karin hotuna a shafinsu na Intanet mai adireshi: www.cartoon-competition.org.


    Mawallafi: Maja Braun | Edita: Umaru Aliyu/MNA