1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai kare muhalli ya dena cin abinci

Abdul-raheem Hassan
May 7, 2024

Wani mai fafutukar kare muhalli a Jamus da ke yajin cin abinci tsawon watanni biyu, ya sha alwashin zafafa zanga-zangarsa har sai gwamnati ta dauki mataki kan masana'antu masu gurbata muhalli a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/4fbXK
Weitere Blockaden von Klima Aktivisten in Berlin
Hoto: Michael Kuenne/ZUMA/picture alliance

Wolfgang Metzler-Kick, mai shekaru 49, ya fara yajin cin abinci a farkon watan Maris na shekarar 2024 da nufin yin zanga-zanga mai taken "Yunwa har sai kun fadi gaskiya". Mutumin ya bi sahun sauran 'yan fafutukar kasar guda uku wadanda ke son matsa lamba ga Shugaban gwamnati Jamus Olaf Scholz ya amince "masifun yanayi na barazana ga rayuwar bil'adama" tare da neman a gaggauta rage hayaki a masana'antu dake fitar da hayaki a nahiyar Turai.

A baya-bayan nan masu fafutukar kare muhalli suna amfani da salo dabam-dabam masu jan hankalin duniya don isar da sakonsu a cii da wajen Jamus, inda suke suke amfani da salon tare manyan titunan ababen hawa da shafa fenti a manyan gine-ginen gwamnati.