1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Chadi: Gwamnatin farar hula ko ta soja

Philipp Sandner MAB/LMJ
May 6, 2024

Al'ummar kasar Chadi na kada kuri'a, domin zaben sabon shugaban kasa da zai kawo karshen shekaru uku na gwamnatin mulkin soja.

https://p.dw.com/p/4fYRK
Chadi | Siyasa | Zabe | Mahamat Idriss Deby | Mulkin Soja | Rikon Kwarya | Takara
Shugaban rikon kwarya na mulkin soja Mahamat Idriss Deby na cikin 'yan takara a ChadiHoto: Gilles Chris Namia Rimbarne/REUTERS

Ga 'yar adawa Lydie Beassemda shida ga Mayu ta kasance muhimmiyar rana ga 'yan Chadi, saboda za su yi amfani da ita wajen juya babin mulkin soja na shekaru bayan mutuwar Idris Deby Itno. Mai shekaru 57 a duniya, ta kasance kallabi cikin 'yan takara 10 da ke zawarcin kujerar shugabancin kasar ta Tsakiyar Afirka. Amma mai yiwuwa ba za ta cika burinta na lashe wannan zabe ba, hasali ma bayan shekaru 30 na mulkin kama-karya a karkashin Shugaba Idriss Deby Itnokasar ta samu sauyin mulki zuwa ga dansa Janar tun bayan rasuwar mahaifinsa a shekara ta 2021 ba tare da tashin hankali ba. Ana dai ganin Janar Mahamat Deby ne zai lashe wannan zaben, kasancewarsa guda daga cikin 'yan takarar shugaban kasar.

Karin Bayani: Afrika na laluben mafita daga ta'addanci

Wannan zaben shugaban kasa na gudana ne a cikin mawuyacin yanayi, inda matsalar tsaro da kasashe makwabta ke fama da ita ta shafi kasar Chadi kai tsaye. Tun daga hare-haren masu rajin kishin Islama a kasashen yankin Sahel na yammacin Afirka zuwa ga yakin da ake fama da shi a kasar Sudan, inda a yanzu haka ma 'yan gudun hijira da suka tsere daga Sudan sun samu mafaka ne a lardunan gabashin kasar ta Chadi. Kasashen Turai da dama na mayar da hankali kan yadda ake ci gaba saboda Chadi ta zama kawa daya tilo da ta rage musu, bayan da Mali da Nijar suka fatattaki sojojin Turai da na Amurka daga kasashensu. Sai dai kungiyoyin da ke dauke da makamai na kai hare-hare a arewacin Chadi, inda ikon gwamnati ya ragu sosai.

Bayani game da zaben Chadi

A halin yanzu ma dai mazauna Arewa na kokawa kan yadda 'yan siyasa suka manta da su a wannan zaben, domin babu dan takara ko daya daga cikin 10 da ya je wannan yanki domin yakin neman zabe. Wani dan kasuwa Younous Ali a garin Miski da ke lardin Tibeti na arewacin kasar, ya ce bai kamata 'yan takarar su mayar da wani yanki saniyar ware ba. Amma a N'djamena babban birnin kasar, an fuskanci kika-kikar siyasa mai tarin yawa a 'yan watannin baya-bayan nan. Da farko dai rikicin da ya barke tsakanin Mahamat Deby Itno da abokan hamayyarsa a karshen watan Fabarairu, ya sa jami'an tsaro kashe  babban mai adawa da shi Yaya Dillo. Masu lura da al'amuran siyasa sun bayyana lamarin a matsayin kisan gilla, sannan wasu daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa sun fuskancin kin amincewar bukatarsu daga kotun tsarin mulkin Chadin.

Karin Bayani: Chadi: An hana wasu 'yan adawa takarar shugaban kasa

Babban mai kalubalantar shugaban gwamnatin mulkin sojan Mahamat Deby da ya rage shi ne Firaminista Success Masra da ya kafa jam'iyyar adawa ta Les Transformateurs, wanda ya jagoranci jerin zanga-zangar adawa da gwamnatin Deby a 2022 da aka kashe daruruwan mutane. Al'ummar Chadi da dama na nuna shakku dangane da dalilin da ya sa Masra ya tsaya takara saboda ya zubar da mutuncinsa bayan da ya amince da mukamin firaminista, lamarin da ya kassara duk fatan adawa na samun nasara a zaben shugaban kasar Chadi. Shi ma dan adawa Saleh Kebzabo da a baya ya amince da rike mukamin firaminista, ya yi gargadin barkewar rudani. Ta  ya ya zaben Chadi zai gudana cikin 'yanci da adalci? Wannan ita ce tambayar da masu lura da al'amura kan dasa, saboda jami'an soja sun shiga yakin neman zaben Janar Mahamat Deby Itno gadan-gadan. Har ma an hango sojojin suna lika fastocin yakin neman zabensa, ciki har da masu rike da manyan mukamai.