1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemi Osinbajo ne mataimakin Buhari

Uwais Abubakar IdrisDecember 17, 2014

Jam'iyyar adawa ta APC ta bayyana sunan Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai wa dan takararta a zaben shugaban kasa janar Muhammadu Buhari mataimaki.

https://p.dw.com/p/1E6Vs
Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Sanar da sunan Farfesa Yemi Osinbajo din dai ya kawo karshen jiran tsammani da ma jita-jitar da aka kwashe tsahon lokaci ana yi a kan wannan batu. A yayin da ya ke jawabin amincewa da wannan takara, Osinbajo da ke da kimanin shekaru 55 a duniya ya ce: "Ina mai godiya ga wannan gagarumar karramawar da aka yi min na zabe na a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyarmu."

Wane ne Farfesa Yemi Osinbajo?

Shi dai Farfesa Yemi Osinbajo kwararren malami ne a fannin shari'a domin kuwa tun daga aikin malanta da ya yi a jami'ar Lagos daga shekara ta 1997 zuwa 1999 inda ya kai ga zama shugaban sashin shari'a na jami'ar. Ya kuma yi aiki a hukumomi da dama har da Majalisar Dinkin Duniya.

Nigeria Oppositionspartei APC
Hoto: DW/K. Gänsler

A fanin shari'ar kanta kuwa Farfesa Osinbajo ya taba zama mai baiwa Atorney Janar na Najeriya shawara daga shekarar 1988 zuwa 1992, sannan a shekara ta 1999 ya zama kwamishinan shari'a na jihar Lagos mukamin da ya rike har zuwa shekara ta 2003. A lokacin da yake rike da mukamin na kwamishinan shari'a Osinbajo ya gudanar da sauye-sauye a wannan fannin musamman tabbatar da kafa cibiyar kula da 'yancin ‘yan kasa da ke samar da wakilci a shari'a ga marasa galihu. Koda yake ana dokin zabensa a wannan mukami, ga Dakta Abubakar Umar Gombe batun ba wai na wanene Farfesa Osinbajo ba ne.

"Maganar ba wai ta Yemi ba ce, ba wani abu na dubi ga waye Yemi, in dai yarjejeniya ce ta Yarabawa suka ce Yemi suke so, to nasan za su tsaya a kai bisa ga gudunmawar da suka bayar tun daga farko har zuwa yanzu."

Wahl Nigeria Proteste
Hoto: DW/U.Abubakar Idris

Wane mizani aka yi amfani da shi wajen zabo Osinbajo?

Shi kuwa janar Muhammadu Buhari mai ritaya dan takarar shugabancin Najeriyar a karkashin Jam'iyyar APC din, cewa ya yi akwai mizanin da suka yi amfani da shi wajen zaben Farfesa Osinbajo a matsayin wanda zai masa mataimaki.

"Akwai mizanin da muka shirya muka sa shugabannin jam'iyya suka tattauna aka bada sunaye da dama kafin a kai ga amincewa da shi."

Kwarewar da Farfesa Osinbajo ke da ita a fannin shari'a, da ta kai shi ga rubuta littattafai da dama da kasancewar sa Kirista, na zama abin da jam'iyyar ke tinkaho da shi da kuma zai zamo sanda abin duka a yayin yakin neman zaben da ke kara zafafa a Najeriyar.