1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: Amfani da EFFC don ceto Naira

February 8, 2024

Bayan share tsawon lokaci tana lallashi, daga dukkan alamu gwamnatin Najeriya ta koma batun saka karfi domin ceto darajar Naira da ke kara durkushewa.

https://p.dw.com/p/4cCCz
Najeriya | Naira | Daraja | Ceto | EFCC
Kokarin ceto darajar Naira da ke kara faduwa a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Ya zuwa yanzu dai daukacin matakan shugabannin Najeriya na shirin gazawa, a kokari na ceton Nairar da ke ta kara yin kasa. To sai dai kuma Abujar na shirin ta daukar tsattsauran mataki, wajen sake daga darajar kudin kasar wato Naira da kuma rage dogaro da kudin kasashen ketare. Hukumar Yaki da Almundahana da Kudin Al'umma ta Najeriyar EFCC, ta kafa wata sabuwar runduna ta musamman da ke shirin daukar ragamar sabon yakin mai tasiri ga makoma ta kasar.

Karin Bayani: Darajar Naira za ta ja baya a 2024 - Bloomberg

Kimanin jami'ai 7,000 aka baza a cibiyoyin hukumar 14 da nufin tunkarar mayar da dalar kudin hada-hada tsakanin al'umma, kuma tuni EFCC din ta ce ta yi nasarar kama da dama a biranen legas da fatakwal a kokarin wankan tsarki cikin hada-hadar kudin mai tasiri. Kama daga biyan haraji  a tashoshin jiragen ruwa ya zuwa kudin makaranta a jami'o'in da ke zaman kansu a Najeriyar ko bayan dillalan filaye da gidaje dai, batun dalar na neman maye gurbin Naira a matsayin kudin hada-hada.

Najeriya | Naira | Dalar Amurka | Zanen Barkwanci
Zanen barkwanci kan darajar NairaHoto: Abdukareem Baba Aminu

Abun kuma da a cewar Dakta Surajo Yakubu da ke zaman kwarrare ga batun halasta kudin haramu, ke neman daukar kasar da mai da ta zuwa rushewa a nan gaba. To sai dai kuma ko ya zuwa ina Abujar ke fatan kaiwa da  nufin cika burin ceton Nairar da ta kai 1,500 kan kowace dalar Amurka, ga dukkan alamu tana bukatar kallo a cikin gida tsakanin 'yan mulki. Kama daga 'yan majalisun tarayya  zuwa gwamnoni dai, kudin dalar na neman maye gurbin Naira wajen batun hada-hada da ma biyan bukata.

Karin Bayani: Sabon tsarin kasuwa ta yi halinta kan hada-hadar kudi

Babban bankin Najeriyar CBN da ke jagorantar yaki da mamayar da dalar Amurkan ke yi a kan kudin kasar wato Naira dai, ya ruwaito cewa dalar Amurka miliyan dubu 98 al'ummar Najeriyar suka kai ga batarwa ko dai  cikin karatu a waje ko kuma neman lafiya da ma yawon bude idanu tsakanin shekara ta 2000 zuwa ta 2020 ko bayan ragowar bukatun cikin kasar da ke shigo da hatta tsinken sakace domin al'ummarta.