1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Farashin dalar Amurka na karuwa a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ/SB/ZUD
October 25, 2023

Tashin gauron zabi da dalar Amurka ke kara yi a Najeriya, ya janyo darajar kudin kasar Naira na kara faduwa kasa wanwar. Ko mai ke haifar da wannan matsala kuma wacce irin illa hakan ke da shi ga tattalin arziki?

https://p.dw.com/p/4Y1bp
Najeriya I Sabon kudin da aka sauya
Kudin Najeriya na Naira da aka sauyaHoto: Ubale Musa/DW

Kasuwar hada-hadar kudin kasashen waje a Najeriyar dai, ta shiga hali na rashin tabbas saboda tsadar da dalar Amurkan ke kara yi kusan bayan kowace sa'a guda farashinta ke canzawa. An shiga wannan hali ne tun bayan da babban bankin Najeriya CBN ya dage haramcin shigo da wasu kayayyaki a kasar, inda a yanzu ake sayar da kowacce dalar Amurka a kan kudi Naira 1,300 kafin ya sauka zuwa 1,270. Masu hada-hadar canjin kudi a kasar dai, sun bayyana cewa fami ne aka yiwa lamarin.

Karin Bayani: Sabon tsarin kasuwa ta yi halinta kan hada-hadar kudi

Dalar Amurka ta zama alamar kudi na duniya
Dalar AmurkaHoto: Joe Giddens/empics/picture alliance

Illa a zahiri da ake gani sakamakon wannan matsala ya sanya majalisar wakilan Najeriyar ta gayyaci gwamnan babban bankin kasar domin neman ba'asi, kamr yadda Hounarable Sada Soli Jibia dan majalisar tarayyar ya tabbatar. Tuni masana tattalin arziki ke kashedin illar da faduwar darajar Naira ke da ita ga tattalin arzikin kasar, musamman 'yan kasuwa da ke sayen dalar domin shiga da kayayyaki. Gwamnatin Najeriya ta bayyana daukar matakai a kan lamarin, a cewar ministan kudin kasar Mista Wale Edun. A yayin da babu alamun samun sauki daga hauhawar farashin dalar Amurkan da rugurgujewar darajar kudin Najeriyar Naira musamman a wannan lokaci da ake fuskantar karshen shekara, lamarin na ci gaba da jefa rayuwar 'yan kasar cikin mawuyacin hali.