1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar al Shabaab ta kai hari a Kenya

Yusuf BalaNovember 22, 2014

Mayaƙan na ƙungiyar sun kai harin ne a garin Mandera da ke a yanki arewa maso gabashi na ƙasar a kan iyaka da Somaliya, a kan wata motar da ke ɗauke da fasinjoji wacce ke kan hanyar zuwa birnin Nairobi.

https://p.dw.com/p/1DreD
AMISOM - Soldaten in Somalia
Hoto: picture alliance/dpa/Jones

Kungiyar mayaƙan sa kai ta al Shaabab na Somaliya ta bayyana cewar harin bam da ta kai kan wata mota safa da ta dauko wasu fasinjoji da ba musulmi ba 28, ramuwar gayya ce kan irin farmakin da 'yan sanda suka kai a wani masallaci da ke birnin Mombasa.

Noah Mwavinda da ke zama shugaban 'yan sanda a yankin ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar matafiya da ba su ji ba, ba su gani ba 28 ne suka mutu a harin.