1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin bayani kan shirin "Tsaka mai wuya"

November 29, 2013

Shiri na musamman da ke taimaka wa yara matasa tattauna abun da suka saurara domin yin nazarin abun da suka ji, domin fara gyara nasu rayuwar tun daga yanzu.

https://p.dw.com/p/1AQ64
LBE-Produktion in Abuja, 2012; Copyright: DW/T. Mösch
Hoto: DW/T. Mösch

Sabon wasan kwaikwayon shirin Ji Ka Karu

A wannan sabon wasan kwaikwayon na radiyo mai zubi biyu kowanne 26, masu sauraro za su hadu da zakarun wasan watau, Hauwa da Mariya sai Ado da kuma Nasir. Dukkan wadannan matasa na haduwa ne a makaranta, sai dai sun fito ne daga rukunoni daban daban na al'umma. Za'a saurari yadda rayuwarsu take gudana a kowane wayewar gari da kuma sakamakon da za su girba daga abunda suka shuka.

" Tsaka mai wuya" shiri ne da ke taimaka wa yara matasa tattauna abun da suka saurara domin yin nazarin kan abun da suka ji, domin fara gyara nasu rayuwar tun daga yanzu. A karon farko shirin Ji Ka Karu zai gabatarwa masu sauraro hotunan bidiyo ta yanar gizo, inda ta nan ne za'a iya sanin ainihin halayyar wasu taurarin wasan kwaikwayon na Rediyo. Duk da matsaloli da suka yi ta shan karo da su, daga karshe Hauwa da Mariya da Ado da Nasir da kuma sauran 'yan wasan, sun cimma kyakkyawar mafita.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani