1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fasahar Samun Nasara a Afirka

Ilimi shi ne ginshikin ci gaban nahiyar Afirka. Sai dai akwai karancin makarantu da jami'o'i. “Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru“ sabon shiri na Deutsche Welle, da zai yi ƙoƙarin matso da ilimi kusa da mabuƙata da ke Afirka.

https://p.dw.com/p/DrEN

Ana samun ci-gaba a harkokin rayuwa a Afrika. Amfani da yanar gizo (Internet) da wayar tangaraho na tafi da gidanka (Mobile) wajen sadarwa, yana daɗa karuwa, sai dai duk da haka har yanzu akwai dubban mutane da aka yanke daga cin moriyar waɗannan na'urori na zamani, dake da nasaba da ci-gaban duniya. Matasan Afirka na ci-gaba da neman gurbi a wannan yanayi, wanda zai jagorance su zuwa samun nasara a irin ayyukan da za su yi, ko kuma irin karatu da za su yi. Alal misali irin wace dama suke da ita na neman ilimi ko kuma karatu ta yanar gizo? Da yawa na tambayan irin dama da suke da ita na cin moriyar wannan sabon yanayi da duniya ke ciki. Kazalika dubban yara matasa na neman yin karatu ta yanar gizo (Online), ko kuma wace irin gajiya sauyin zamanin yanzu zai samar musu.

Ilimantarwa da nashaarwa

Tashar Deutsche Welle na son kawo sauyi. Shiri Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru, zai kalubalanci waɗannan matsaloli ta hanyar ilimantarwa da nishaɗantarwa. Za a gabatar muku da shirye-shirye da suka haɗa da rahotanni, wasannin kwaikwayo na rediyo da shirye-shiryen nishaɗantarwa. Shirin Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru, zai taimaka wa masu sauraro samun fasahar zamani domin cimma nasaraganin 'yan Afirka na tafiya tare da wannan zamani. Rukunin mutanen da shirin ke son isar da saƙon gare su, sune 'yan mata da samari da ke tsakanin shekaru 12 izuwa 25 da haifuwa.

Abokanen hulɗa

Marubuta daga nahiyar Afirka ne za su shirya waɗannan shirye-shirye tare da haɗin kan ma'aikatan Deutsche Welle. Za a iya samun shirin Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru a ko'ina cikin harsuna masu yawa: Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, harshen Portugal da harshen Habasha.