1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Tchangari da alaka da Boko Haram

Abdoulaye Maman Amadou/GATMay 21, 2015

Gwamnatin Nijar ta zargi Musa Tchangari na kungiyar kare hakkin Dan Adam ta Alternative da hada baki da kungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1FTrX
Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler
Hoto: DW/ Thomas Mösch

A karon farko tun bayan da jamian tsaro, masu yaki da aiyukan ta'addanci suka dakatar da fitaccen dan gwagwarmayar nan na kungiyoyin fararen hullar Alternative Malam Musa Tchangari, a ranar 18 ga watan nan, hukumomi sun fito sun bayyana abin da suke zargin shi da shi.

Gwamantin kasar dai na zargin Musa Tchangari ne da hadin baki da yawan ambaton kalaman da basu da tushe a yakin da kasar take yi da 'yan kungiyar Boko Haram, da kuma bayyana wasu kalaman tozartawa ga jami'an tsaron kasar, inji Ministan harkokin cikin gidan kasar a wata sanarwa da aka wallafa mai dauke da sa hannunsa a kafafen yada labarun kasar.


A yayin wata firar da kamfanin dillancin labarun AFP na kasar Faransa da aka wallafa a kafafen yada labaru mallakar gwamnati dai ne ministan na cikin gida ya ambaci zarge- zargen da hukumomin kasar ke yi wa Malam Musa Tchangari.

Musa Tchangari ya yi kwanaki uku a kulle

Ana dai tuhumar Tchangari ne da gamin baki da ambato kalamai maras tushe masu alaka da Boko Haram, zargin dai da hukumomin suka wallafa na zuwa ne a yayin da Musa Tchangari ya shafe kwanaki uku a hannun jamian tsaro, kamen da tuni wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama na gida da waje suka fara zargin na da nasaba ne da hana tofa albarkacin bakinshi game da abinda ke faruwa, wanda
hakan na daga cikin al
amurran da suka sabawa dokokin kasa da kasa.

DW im Niger Yahouza Sadissou Mabobi
Ministan yada labarai na kasar Nijar ya kare matakin gwamnati na tsare TchangariHoto: DW/M. Kanta

Sai dai ministan yada labarun kasar ta Nijar Malam Yahuza Sadissou ya ce wannan ba hujja bace:


"Dokar ta baci bata nufin hanawa wane ko wane fadin abinda yake so, aa idan zaka fadin albarkacin bakinka kada kayi karya kada kayi karya kada kada kayi zargi kada kayi karya ba hujja ba ce a tozarta sojojinmu a nuna cewar sojojinmu bas u da ko wani kwazo ko kwarin gwiwa aa ba hijja bace idan an zo an yi bincike su ka gano bincikensu to su zo su kawo hujjojinsu gwamnati tayi nazarinshi ta duba ta gani idan har binciken gaskiya ne ko wannan binciken gaskiya ne ko karya ne"

To amma sai dai kungiyoyin na fararen hullar da suka yi tir da allah wadarai da kamun na Musa Tchangari sun fito fili domin kara nuna rashin gamsuwarsu kan zarge-zargen da gwamnatin ta ce tana yiwa Tchangari a matsayinsa na 'yan kungiyoyin fararen hulla. Nuhu Muhamadu Arzika jigo ne a cikin kungiyoyin fararen hullar Jamhuriyar Nijer:


"Dole ne idan mun ga ana yi ba dai-dai ba sai mu fadi domin yau baa fitowa a ce kuma mu ne muke neman mu hana abinda ake son a yi a cikin kaida idan ko aka wuce kaida, aka wuce hanya wajibi ne mu ce an wuce gona da irin kuma shi ne Musa yayi mu ma shi ne muke yi idan haka nan ne ba Musa daya ne ba har mu ma sai an kama, to yaya kukaji da wannan zargin yo daman wannan zargin wanda yayi shi daman ya saba."

Soldaten im Niger
Gwamnatin Nijar na kira ga kara kawo goyan baya ga sojojin kasar cikin yaki da Boko HaramHoto: Desmazes/AFP/Getty Images

Kamen abin mamaki ne ga kungiyoyin fararen hula
Ko baya ga Nuhu Muhamadu Arzika tuni wasu takwarorin Musa Tchangari suka nuna mamakinsu kan zarge-zargen da gwamnatin ta ce tana yi masa. Mustapha Kadi Umani na daya daga cikin masu cike da mamakin:


"Yaya ne wai yau zaa ce don dan kungiyoyin farar hulla ya ce ma gwamnati tayi hattara ki bi hanyar doka sai a ce a'a son ake kowa yayi shuru mutane suyi hankali da sharri domin wannan yakin fa bai kamata ya rarraba kawunan mu b ayan Nijer."


Yanzu hakan dai kungiyoyi kamar su Amnesty International da FIDH OMCT daukacinsu suna tir da allah wadarai da kamun, tare da neman a sako shi cikin gaggawa.