1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman lafiya a Afirka na da muhimmanci ga Turai

April 4, 2014

Bukatu iri daya suka hada nahiyar Turai da nahiyar Afirka da ke zama babbar makwabciyar Turai a sashen kudu.

https://p.dw.com/p/1BcDg
EU Afrika Gipfel Merkel 02.04.2014 Brüssel
Hoto: Reuters

Za mu fara sharhin jaridun ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda albarkacin taron kolin tarayyar Turai da kasashen Afirka da ya gudana a wannan makon a birnin Brusels, ta rawaito ministocin tsaron kasashen Jamus Ursula von der Leyen da takwararta na Faransa Jean-Yves Le Drian suna magana game da muhimmancin daidaituwar al'amura a Afirka.

"Rashin tsaro Afirka na naufin rashin tsaro a Turai. Kuma ba za a samu ci gaba a Afirka ba idan babu tsaro a wannan nahiya, saboda haka muradu iri daya ne suka hada nahiyar Turai da nahiyar Afirka da ke zama babbar makwabciyar Turai a yankin kudu. Jaridar ta ce Afirka nahiya ce mai dinbim matasa da ke da kyakkyawar makoma a fannin bunkasar tattalin arziki. Sai dai rikice-rikice a sassa daban daban na nahiyar na nuni da yadda zaman dar-dar ke karuwa a wasu kasashenta wanda kuma ke barazana ga sha'anin tsaro. Alal misali ayyuka tarzoma a yankin Sahel sun kasance babbar barazana ga harkokin tsaro a Afirka da kuma Turai. Saboda haka harkar tsaro da kuma matakan riga-kafi sun kasance cikin muhimman batutuwan da taron kolin shugabannin Afirka da na Turai ya mayar kai."

Cece-kuce kan annobar Ebola

Ebola in Guinea MSF Mitarbeiter in Schutzanzügen
Ma'aikatan kungiyar likitoci ta duniya a GuineaHoto: MSF

Har yanzu annobar cutar Ebola da ta bullo a kasar Guinea na ci gaba da daukar hankalin wasu jaridun Jamus irinsu jaridar Berliner Zeitung, wadda ta rawaito wata takaddama tsakanin hukumar lafiya ta duniya WHO da kungiyar likitoci masu ba da agaji a kan hatsarin cutar ta Ebola.

"Yayin da kungiyar Medicin Sans Frontier ta ce cutar Ebola da ta bulla a kasar Guinea da kuma kasashen Liberiya da Saliyo na yammacin Afirka da wata annoba, ita kuwa hukumar WHO cewa ta yi a yi hattara da yadda ake kwatanta barkewar cuta da kawo yanzu ta shafi daidaikun mutane. Daga cikin mutane 120 da suka kamu da kwayoyin cutar ta Ebola, akalla 80 sun kwanta dama. Tuni dai wasu kasashen yankin yammacin Afirka sun dauki matakan riga-kafi. Annobar Ebola mafi muni ta auku ne a shekarar 1995 a kusa da garin Kikwet na kasar Kwango, inda ta hallaka mutane 245. Cutar ta dai fi barkewa a yankunan kurmi na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Gabon da Kwango da kuma Yuganda."

Zaman zullumi a Kenya bayan kisan wani malami

Abubakar Shariff Ahmed
Abubakar Shariff AhmedHoto: picture alliance/AP Photo

Karuwar zaman dar-dar na addini a Kenya inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai nuni da kisan wani mai wa'azin Musulunci a birnin Mombasa a ranar Talata da ta gabata.

„Wasu da ba a gane su ba sun hallaka Abubakar Shariff Ahmed da aka fi sani da suna „Makaburi“. Malamin shi ne na uku a jerin malaman da ke wa'azi a masallacin Musa da ke birnin na Mombasa da aka kashe a kasa da shekaru biyu. A cikin watan Agustan 2012 an hallaka magabacinsa Sheikh Abud Rogo, abin da ya janyo tarzoma ta tsawon kwanaki da magoya bayansa. A cikin watan Oktoban bara an kashe magajinsa Ibrahim Isma'il. Abubakar Sharif Ahmed ya zargi jami'an tsaro da hannu inda ya ce shi ma ko ba jima ko bade hakan ka iya cikawa da shi. Kisan na wannan malamin ya zo ne a wani lokaci da aka daura danban yaki da ta'addanci da kuma karuwar zaman zullumi na addini. A ranar Litinin akalla mutane shida sun rasu sakamakon hare-haren bam guda uku a unguwar Eastleigh ta 'yan Somaliya da ke birnin Nairobi. Wani abin damuwa shi ne bankado wani yunkurin kai harin ta'addanci a birnin Mombasa. Sannan a makon da ya gabata wani dan Somaliya ya rasu lokacin da yake kokarin dana bam a Nairobi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar