1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben 'yan majalisar dokoki a Ethiopia

Gazali Abdou TasawaMay 22, 2015

'Yan adawa na fargaba da sahihancin sakamakon zabe a yayinda matasa ke neman samun wakilci a fagen siyasar kasar Ethiopia .

https://p.dw.com/p/1FUOy
Äthiopien Wahlen 2015
Zaben Ethiopia na 2015Hoto: DW/E. Bekele

A wannan Lahadin ce al'ummar kasar Ethiopia ke gabatar da zaben sabbin 'yan majalisar dokoki. Cikin masu taka rawar gani a wannan karon har da jam'iyyar gwamnatin hadaka ta EPRDF, wadda ke mulkin kasar tun daga shekara ta 1991

Bisa ga dukkan alamu dai ba zata sauya zani ba a danagne da zaben 'yan majalisar dokokin na kasar Ethiopiya, duk da cewar akwai sabuwar jam'iyyar adawa da zata yi takara daura da sauran na da. Jam'iyyar Semayawi dai na mai kasancewa jaririyar jam'iyyar adawa, wadda ke nufi kalar ruwan bula a harshen Amharik, launin dake da nasaba da muradun jama'ar Ethiopiya wanda kuma ake dangantawa da juyin juya- halin daya jagoranci guguwar sauyi a kasashen larabawa.

Matasa na bukatar samun matsayi a fagen siyasa

Äthiopien vor der Wahl EPRDF Anhänger in Addis Abeba
Wani matashi na farfagandaHoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Duk da tsaurara matakan tsaro na gwamnati dai jam'iyyar ta jagoranci gangamin lumana da ya janyo dubban mutane zuwa titunan kasar. Ko mene ne ya janyowa sabuwar jam'iyyar ta Semayawi wannan irin farin jinin?Yilkal Getnet shi ne babban sakataren Jam'yyar....

" Akasarin shugabannin siyasa kama daga wadanda suke cikin gwamnati ko kuma bangaren 'yan adawa suna da tsoffin akidojin siyasa. Amma wanna kasa ce ta matasa, kashi 70 daga cikin 100 na al'umma Ethiopiya matasa ne da shekarunsu basu shige 35 ba. Kuma ya zamanto wajibi wannan rukuni na mutane su samu wakilci a fagen siyasa. Sa'annan muna muradin samun sabon babi a fagen fafutukar siyasa, tare da nuna hazaka da basira da sanin yakamata".

Da wannan furuci dai akwai alamun cewar kofa ta budewa matasa masu jini a wuya, wadanda ba'a lissafinsu cikin albarkatun wannan kasa, domin samun damar yin takara da ma kada kuri'unsu. Nan da shekara ta 2015 dai, kasar ta Ehiopia zata shiga jerin kasashe masu matsakaita kudaden shiga kamar Masar da China. Daga nan ne kuma za ta yi hankoron samun mataki na gaba cikin shekaru biyar masu zuwa, wanda shine kashin bayan hadakar jam'iyyun hudu da ke mulkin kasar tun daga shekara ta 1991.

A kwanan ne dai gwamnatin kasar ta ke bukukuwan kaddamar da layin dogo na miliyoyin euro. Birnin Adisababa da ke zama fadar gwamnatin kasar dai ta kasance makil da shaguna da hada- hadar yau da kullum. Sai dai akwai matsalar tsadar farashin kayyayaki a yayin da matasa kasar ke fuskantar barazanar rashin aikin yi baya ga karancin matsugunnai da ake fuskanta.

Tauye 'yancin aikin jarida a Ethiopia

Daura da wannan Ethiopiya ta yi kaurin suna wajen take hakkin al'umma. 'Yan jarida dai basu da tacewa a wannan kasa, inda ta kasance a matsayi na hudu na kasashe 10 da aka fi gallazawa 'yan jarida a duniya, baya ga kamen masu adawa da gwamnati ko kuma fafutukar kare hakkin al'umma. Dr Awol Allo mai bincike ne kan kare hakkin jama'a a Ethiopia a makarantar nazarin harkokin tattali dake birnin London....

Äthiopien vor der Wahl EPRDF Anhänger in Addis Abeba
yan jarida na zanga-zangar neman 'yanciHoto: Reuters/Tiksa Negeri

" Ko shakka babu a bayyana take cewar kasar Ethiopia na samun bunkasar tattalin arziki, sai dai alokaci guda kuma akwai gwamnati mai musgunawa jama'a, wadda ko kada ba zata daga kafa wa dukkan wanda ya yi mata suka ba, kama daga 'yan jam'iyyun adawa, 'yan jarida, marubutan fafutuka a yanar gizo da ake kira Blogger da masu magana da yawun al'umma. Don haka bana ganin wadannan abubuwa ne da ke da alaka da juna".

Kungiyar Tarayyar Turai wadda ita ce babbar mai bada tallafin raya kasar ta yi fatan zaben zai gudana a cikin adalci da lumana, sabanin na shekara ta 2005 inda aka yi asarar rayukan masu gangamin adawa da sakamakon zaben 200.