1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Tunisiya

November 23, 2014

Al'ummar kasar Tunisiya sun fita a ranar Lahadin nan dan kada kuri'a a zaben shugaban kasa karon farko tun bayan juyin juya hali a shekarar 2011 da yayi sanadin tada guguwar sauyi a tsakanin kasashen Larabawa.

https://p.dw.com/p/1DrqK
Bildergalerie Präsidentenwahlen Tunesien
Hoto: Getty Images/Afp/Fethi Belaid

Zaben da ake ganin zai samar da sauyi a turka-turkar siyasar wannan kasa da ke kan hanyar kafa cikakkiyar Demokradiya.

Cikin wadanda suka shiga a fafata da su a 'yan takarar shugabancin wannan kasa, sun hadar da tsohon Firemiya Beji Caid Essebsi dan shekaru 87 da jam'iyyarsa ta Nidaa me nesanta kanta da addini ta samu nasara a zaben 'yan majalisar dokoki a watan da ya gabata.

Sauran da suke cikin wannan takara sun hadar da Muhammad Moncef al-Marzouki da ya rike kujerar gwamnatin rikon kwaryar wannan kasa ta Tunisiya , da ma wasu ministoci da dama da suka rike madafun iko a lokacin gwamnatin kama karya ta Zine El Abidine Ben Ali.

Fiye da mutane miliyan biyar ne a wannan kasa suka cancanci kada kuri'a inda aka tanadi dubban jami'an tsaro da suka hadar da 'yan sanda dan sanya idanu su tabbatar da ganin an gudanar da zaben ba tare da tashin hankaliba.

Da misalin karfe biyar na yammaci agogon GMT ne za a kammala kada dukkan kuri'un a mazabu.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu