1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Mozambik ya bar baya da kura

October 17, 2014

Madugun 'yan adawa Afonso Dhlkama ya ki amincewa da shan kaye a zabe . Lamarin da ke barazana ga zaman lafiya a fadin Mozambik, a cewar sharhin Johannes Beck.

https://p.dw.com/p/1DX4b
Wahlen Mosambik 15.10.2014 Afonso Dhlakama
Hoto: AFP/Getty Images/Gianluigi Guercia

Sharhin ya fara da cewar alkaluma sun nunar da cewar jam'iyyar FRELIMO da ke mulki ta lashen zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Mozambik. Sai dai kuma Jam'iyyar RENAMO da ke adawa ta yi watsi da sakamakon zaben, sakamakon zargin magudi da ta ke yi. Lamarin da ya zo wa RENAMO a ba zata, wanda kuma zai iya kawo ruduni a kasar.

Farin jinin madugun 'yan adawa Afonso Dhlakama ya ragu a tsakanin 'yan kasarsa tun shekaru biyar da suka gabata, saboda sun daina daukarsa a matsayin shugaban tsofuwar kungiyar 'yan tawaye ta RENAMO. Maimakon haka suna daukanshi a matsayin kadangaren bakin tulu ga jam'iyyar FRELIMO da ke mulki. Da yawa daga cikin 'yan Mozambik na danganta Dhlakama da wata barazana ga zaman lafiya, saboda zai iya sake daukan makamai domin tayar da kayar baya.

Hasali ma dai, Dhlkama ya yi wa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tun shekaru 20 da suka gabata karar tsaye. ya shiga takun saka da 'yan sanda da sojoji da kuma ita kanta gwamnatin Mozambik. Ko da shi dai ya mayar da takobinsa a watan Agusta na shekarar da ta gabata, amma kuma wannan rikici ya lamshe rayukan mutane 54 ciki kuwa har da fararen hula da ba su ci buzu ba, suka yi aman gashi.

Wahlen Mosambik 15.10.2014 Daviz Simango
Daviz Simonga na jam'iyyar MDM ya zama raba gardamaHoto: DW/A. Sebastiao

Tushen rikici tsakanin RENAMO da FRELIMO

Sai dai kuma tayar da kura da Dhlkama ya yi a kan FRELIMO da ke mulki da kuma wadanda ke wawushe arzikin karkashin kasa da Allah ya hora wa Mozambik, ya bayar da damar susa wa da yawa daga cikin 'yan kasar inda ya ke yi musu kaikayi. Wasu daga cikin 'yan Mozambik na daukansa a matsayin wanda zai iya tsame kasar daga halin da ta ke ciki, tare da ciyar da ita gaba. kowa ya yi ammanar cewar rawar da zai taka a zaben Laraba za ta zarta na shekaru biyar da suka gabata.

Amma kuma da dama an sai cewar da kamar wuya Dhlkama ya kai ga kayar da dan takara Filipe Nyusi na FRELLIMO da ke mulkin Mozambik. Dalili kuwa shi ne, Ya ki damawa da jam'iyyar adawa ta MDM, wanda shugabanta Daviz Simango ya raba gari da RENAMO a shekarun baya saboda adawa da ta ke yi da karfin da ta ke amfani da shi. Ita jam'iyyar MDM ta samun angizo a zaben kananan hukumomi na Nowamban da ya gabata, wanda RENAMO ta ki shiga a dama da ita.

Barazanar tashin hankali kamar a 1999

Mozambik na fusknatar barazanar fadawa cikin tashin hankali kamar wanda ya gudana bayan zaben shekarar 1999. A wancan lokaci dai, madagun 'yan adawa Afonso Dhlkama ya sha kaye a zaben da ya gudana, ko da shi ke masu sa ido sun bayyana cewar ya na cike da kura-kurai. Mutane sama da 40 ne suka rasa rayukansu a wannan tashin hankali.

A wannan zabe na shugaban kasa da na majalisa da ya gudana a ranar Laraba ma dai, an samu korafe-korafen tafka magudi musamman ma a yankunan da 'yan adawa ke da goyon baya. A lardunan Nampula da Sofala da kuma Zabezia, an bude runfunan zabe da lati, baya ga rashin kai takardun kada kuri'a a kan kari. Lamarin da ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin sassa biyu.

Dole ne bangaren FRELIMO da ke mulkin Mozambik da kuma RENAMO mai adawa su yi karatun ta nitsu. Ya kamata Afonso Dhlakama ya yi amfani da hanyoyin da dokoki suka amince da su wajen neman hakkinsa, musamman ma idan aka yi la'akari da cewa jam'iyyarsa ta RENAMO ta ce ba za ta amince da sakamakon zabukan ba saboda an tafka magudi a cikinsu.

Wahlen Mosambik 15.10.2014 Filipe Nyusi
Filipe Nyusi ne FRELIMO na kann gaba a zaben MozambikHoto: DW/A. Cascais

Shi kuwa Dan takarar FRELIMO wato Filipe Nyusi ya wajabta a kansa ya yi sara ya na duba bakin gatari, ma'ana ya magance kura-kuran zabe, ta hanyar shirya wanda zai samu karbuwa ga kowa da kowa. Sannan kuma ya kawo karshen amfani da arzikin karkashin kasar Mozambik da kusoshin gwamnati ke yi wajen azirta kansu. Ta wadannan hanyoyin ne kawai Mozambik za ta iya shiga sahun kasashen da ake zaman lafiya, wadanda kuma mulkin demokaradiya suka fara tsayawa da kafafunsu.

Mawallafi: Johannes Beck
Edita: Mouhamadou Awal