1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi kwaskwarima ga dokar zabe a Najeriya

August 21, 2014

Kungiyoyi masu zaman kansu na son a gyara dokar zabe musamman amfani da jami’an tsaro a lokutan zabe a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1CyPg
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Wannan mataki da ake ganin na zama kama hanyar kai wa ga samun amincewa da yi wa dokokin zaben Najeriyar gyaran fuska da majalisar ta ke yi, damace garesu domin amayar da abubuwan da ke ransu a game da dokar zaben kasar da suke ganin tana bukatar a sake yi mata saiti kafin zaben 2015. Dr Yunusa Tanko shine shugaban majalisar bada shawara ta jamiyyun siyasa kuma jagora ga jamiyyar adawa ta NCP ya bayyana wasu abubuwan da suke bukata a yi masu gyara.

‘'Misali akwai dokar nan wacce da zarar mutunm yaci zabe a wata jam'iyya haka nan kawai sai ya canza sheka, wannan baya yiwuwa, ko kuma a ce a baiwa wasu jamiyyun kalilan ikon suna diban dukiyar kasa suna harkokin nasu jamiyyun amma kuma wasu an hanasu, in an haka ne za'a samu sahihin zabe. Kuma a lokacin da ake cewa su jam'iyyun nan menen tasirinsu a Najeriya, to gyran fuskan da za'a yi shine zai bai wa jamiyyun nan tasirinsu har su kai ga cin zabe a kasar ''.

Duk da cewa an dade da watsi da yunkurin kara wa'adin mulki, ga masu rike da mukamman siyasa, amma har yanzu batun sauya dokar ikon tsaida dan takara daga jamiyyun siyasa zuwa ga hukumar zabe na cikin batutuwan da ake dubawa. Amma ga kungiyoyi masu zaman kansu batun, amfani da jami'an tsaro a wajen zaben ne yafi daukan hankalinsu.

Goodluck Jonathan Wahlen in Nigeria
Hoto: AP

Ganin jamiyyar PDP ta turo wakilinta a zaman da aka gudanar ya sanya tambayar har da su da ke rike da madafan iko, nada korafi abinda suke son a yi wa gyara? Barrister Bashir Maidugi shine mataimakin mai bai wa jam'iyyar PDP shawara a fanin shari'a.

‘'Sosai saboda duk abubuwan da muke ganin ya kamata a gyara mun riga mun aiwatar da su kuma ya kamata a yi gyaran da ya kamata a yi, dama can ai sun taba yin gyaran kuma yanzu ma za'a yi, bayan zaben ma za'a sake yi don ba abu ne na kwana daya ba, saboda a samu nasara a samu doka mai kyau wacce zata kunshi komai da komai''

Aikin gyaran fuska ga dokokin zaben Najeriyar dai ya kasance wanda ya dade yana fuskantar kwan gaba kwan baya musamman saboda tsawon lokaci da ‘yan majalisun suka dauka. To sai dai jama'a da dama na jefa shakku a kan yiwuwar aikin, musamman saboda kurewar lokaci ga majalisar dama zaben da ya kawo jiki.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris daga Abuja
Edita : Yusuf Bala