1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin tsige Shugaba Jonathan

Uwais Abubakar IdrisNovember 26, 2014

Wasu ‘yan majalisar dattawan Tarayyar Najeriya sun fara shirin tsige shugaban kasar bisa zargin sa da karya dokokin kundin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/1DuG9
Nigeria Präsident Goodluck Ebele Jonathan
Hoto: imago/Wolf P. Prange

'Yan majalisar dattawan sun kuma yi Allah wadai da kutsen da 'y an sanda suka yi a majalisar, yayin da aka waste baram-baram tsakanin kwamitin majalisar wakilai da sifeto janar na ‘yan sandan kasar a lokacin da ya bayyana a gabansu domin amsa tambayoyi. Majalisar dai ta kwashe lokaci mai tsawo inda ta tattauna a kan kutsen da ‘yan sandan Najeriya suka kai a majalisar wanda suka ce babbar barazana ce da dole su bincika. A dangane da haka ne suka kafa kwamiti mai wakilai bakwai karkashin jagoranci Sanata Ahmed Makarfi domin bincika lamarin. To sai dai a mafi yawan lokuta kafa kwamiti na zama karshen maganar kenan. Ko me Sanata Ahmed Lawan zai ce don kada aikin nasu ya zama na baban giwa?

Sifeto janar na 'yan sandan Najeriya Suleiman Abba
Sifeto janar na 'yan sandan Najeriya Suleiman AbbaHoto: DW/U. Musa

Kwamitin na fatan yin aikinsa

"To bari mu yi fatan wannan kwamitin zai yi aikinsa, kuma in ya yi majalisar za ta amince da aikin ta mikawa shugaban kasa, sai dai ba a nan gizo ke sakarsa ba, domin duk abinda za'a yi za'a ce 'yan sanda basu yi dai dai ba, sai an aikawa shugaban kasa. Kaga a nan sai abinda ya yi, zasu iya yin abinda suka saba amma dai bari mu yi aikinmu mu yi fatan fadar shugaban kasa zasu kalli abin kamar yadda muka yi."

A yayin da majalisar dattawan da dage zamanta har zuwa 22 ga watan Disamba mai kamawa tuni wasu 'yan majalisar suka fara daukar matakin tsige shugaban Najeriyar Goodluck Ebele Jonathan bisa abinda suka kira laifuffuka na karya dokokin tsarin mulkin kasar. Sanata Alkali Jajere ya ce shima ya sanya hannu kan takardar yunkurin tsige shugaban kasar da tuni ‘yan majalisar wakilai suka yi nisa a kansa.

Baran-baran a majalisar wakilai

A can majalisar wakilan Najeriya kuwa bayyanar da sifeto janar na 'yan sandan Najeriyar ya yi a kwamitin kula da harkokin 'yan sandan kasar bai zo da dadi ba domin hayaniya ta tashi a kan kin amincewar da sifeton ya yi da ya kira sunan shugaban majalisar Aminu Waziri Tambuwal da sunansa, inda suka yi uwar watse. A jawabinsa sifeto janar din 'yan sandan Suleiman Abba ya bayyana dalilan kutsen da 'yan sanda suka kai a majlisar yana mai cewa.

Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aikiHoto: imago/Xinhua

"Game da amsar barkonon tsohuwa da aka ce an jefa, babu shakka abin takaici ne, kuma ta fashe ne a kofar shiga majalisa kuma ana bincike akan wannan batu, amma fa mun ga yadda aka karya tsarin tsaro mun ga wadanda muka yi zaton 'yan banga ne suka tsallake shingen shiga majalisar."

Sai dai amsar ta sa ta fusata 'yan majalisar inda wani mamab a majalisar Shu'aibu Gwanda Gobir ke cewa basu gamsu da amsar da ya basu ba ko kadan.