1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin magance mutuwar bakin haure

Ahmed SalisuApril 27, 2015

Kasashen EU na tunanin amfani da karfin soji wajen dakile aiyyukan masu fasa kaurin mutane daga nahiyar Afirka zuwa Turai ta tekun Bahar Rum.

https://p.dw.com/p/1FEWh
Symbolbild - Flüchtlingsboot Mittelmeer
Hoto: Marco Di Lauro/Getty Images

Kasashen na EU musamman ma Burtaniya da Faransa sun yanke wannan shawara ce a wani taro da mambobin kungiyar tarayyar Turai suka yi da nufin kawo karshe wannan ibtila'i na mutuwar daruruwan bakin haure da ake samu daga lokaci zuwa lokaci a yunkurinsu na shiga nahiyar Turai don samun kyakkyawar rayuwa.

A shi wannan zama da suka yi, EU din ta amince ta rubanya irin kudin da ta ke badawa wajen nema da bada agajin gaggawa ga jiragen ruwan bakin haure da kan samu hadari a tekun na Bahar Rum. Ita kuwa Burtaniya cewa ta yi za ta bada jiragen ruwa na yin sintiri da jiragen sama masu saukar ungulu don yin amfani da su a Tekun na Bahar Rum sai dai ta ce hakan ba ya na nufin za ta bada mafaka ga wanda aka ceto a kasarta kai tsaye ba.

Shugaban hukumar gudanarwar EU din Donald Tusk ya ce ba a nan abin zai tsaya ba don kuwa sun amince da bijiro da wani shiri na musamman don cimma nasarar da aka sanya a gaba ''shugabanni sun bukaci wakilansu da su fidda wani tsari da za a yi amfani da shi wajen kamawa da lalata jiragen ruwan masu safarar bakin haure kafin ma su kai ga hawa kan teku. Yayin yin hakan za a yi amfani da dokoki na kasa da kasa da kuma kiyaye 'yancin bani Adama.''

Libyen Migranten im Abu Salim Zentrum
Kasashe na muhawara kan makomar bakin hauren da ake samu.Hoto: picture-alliance/dpa

Faransa ma dai na ra'ayin lalata jiragen masu safarar bakin haure bisa amfani da hanyoyin da doka ta shardanta sai dai shugaban kasar Francois Hollande ya ce matslar fata fi gaban ta bakin haure don kuwa 'yan ta'adda na iya amfani da wannan hanya ta shiga Turai don yin aika-aika a wasu kasashen. Shugaba Hollande ya ce ''mafi muni da wata kila zai iya faruwa nan gaba shi ne samun wata tunga ta 'yan ta'adda a Libya don haka ba wai jiragen ruwa na bakin haure ba ne kawai za su iya isa kasashen Turai, har ma da na 'yan ta'adda don haka dole ne mu tashi tsaye kuma ba wai Turai ce kadai za ta yi aikin ba dole ne kasashen duniya su dafa.''

Italien Migranten
Bakin haure kan yi amfani da kananan jiragen ruwa dan shiga TuraiHoto: picture-alliance/dpa/Italian Navy Press Office

Ita kuwa Italiya a nata bangaren fata ta yi na ganin kudurin Burtaniya da Faransa ya samu haye a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don samun sukunin kawo karshen wannan matsala yayin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ke fatan ganin an yi wannan aiki bisa sharuddan da aka tsara ciki kuwa har da mutunta 'yanci na bani Adama.