1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar tsige shugaban kasa a Najeriya

Lateefa/Uwais Abubakar IdrisNovember 20, 2014

Majalisar wakilan Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta fara tattauna batun tsige Shugaba Goodluck Jonathan, a dai-dai lokacin da yake neman amincewarsu domin tsawaita dokar ta-baci.

https://p.dw.com/p/1Dqfa
Nigeria Parlamentspräsident Aminu Tambuwal
Hoto: picture alliance/Photoshot

Majalisar wakilan ta kuma sanar da kawo karshen dokar ta-baci da aka sanya a jihohi uku da ke yankin arewa maso gabashin kasar, inda ta ce ta yi watsi da bukatar da shugaban kasar ya mika wa majalisun dokokin kasar na su amince da kara wa'adin dokar da jihohin suka kwashe tsahon watanni 18 a karkashinta. Mai magana da yawun majalisar wakilan Zakaria Mohammed ne ya tabbatar da hakan inda ya kara da cewa a iyakacin saninsu dokar ta-bacin da gwamnati ta sanya a jihohin Adamawa da Borno da Yobe ta kawo karshe.

Sojojin Najeriya da suka mamaye yankin arewa maso gabashin kasar
Sojojin Najeriya da dama na aiki a yankin arewa maso gabashin kasarHoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye

Wannan mataki na majalisar na zuwa ne bayan da jami'an 'yan sandan kasar suka yi yunkurin hana shugaban majalisar wakilan da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC Aminu Waziri Tambuwal da wasu mambobin majalisar shiga harabar majalisar ta hanyar fesa musu hayaki mai sa hawaye. Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sandan sun kuma rufe kofar shiga majalisar, wanda hakan ya sanya mambobin majalisar suka rinka haurawa, kafin daga bisani 'yan sandan su fesa musu hayaki mai sa hawaye. Wannan lamari dai ya tunzura 'yan majalisar dokokin Najeriyar, inda har ma suke tunanin fara tattauna batun tsige shugaban kasa Good Luck Jonathan da a yanzu haka ya yi balaguro zuwa kasar Ingila.

Yanke shawar ba tare da kada kuri'a ba

'Yan majalisar dai basu kada kuri'a kan batun tsawaita dokar ta-bacin ba, kuma sun yanke shawarar yin fatali da bukatar Shugaba Jonathan na Najeriyar ne a wani taron sirri da suka gudanar. A yanzu haka shugaban majalisar dattawan kasar ya bukaci da a rufe majalisar har sai nan da mako mai kamawa sakamakon hatsaniyar da ta faru a majalisar, yayin da a hannu guda kuma majalisar wakilan ta ce ta san matakin da za ta dauka. Masu fashin baki dai na ganin dokar ta-bacin ta tsahon watanni 18 ba ta tsinana komai a wadannan jihohin ba sai ma kara ta'azzara al'amura da ta yi.

Kungiyar Boko Haram da ta kwace garuruwa da dama a yankin arewa maso gabashin Najeriya
Kungiyar Boko Haram da ta kwace garuruwa da dama a yankin arewa maso gabashin NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo