1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya lokacin zabe

Ubale Musa/PAWMarch 26, 2015

Manyan jam'iyyun Najeriya biyu da kuma 'yan takarar da ke musu jagora sun dauki alkawari na mutunta sakamakon zaben komai daci.

https://p.dw.com/p/1Ey9E
Nigeria Goodluck Jonathan Abdulsalami Abubakar Muhammadu Buhari
Hoto: DW/Ubale Musa

A wani taron da ya samu halartar manyan yan kwamitin tabbatar da sake zaman lafiya da safiyar yau a Abuja dai shugaban kasar Goodluck Jonathan da kuma Janar Muhammadu Buhari da ke jagoranta ga adawa sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar tabbatar da zaben a cikin masalaha sannan kuma da amincewa da sakamakon da zai fito a cikinsa.

Shugabannin biyu da kuma shugabannin jam'iyyun nasu gamIida 'ya'yan wani kwamiti na tabbatar da zaman lafiya yayin zaben dai sun share kusan mintuna 25 suna ganawar sirri kafin daga baya su fito ga jaridu don baiyyana sabuwar yarjejeniyar dake zaman tabbaci na karshe a tsakanin bangarorin biyu. Bishop Hassan Mathew Kukah dai na zaman dan kwamitin da kuma ya karanta sabuwar yarjejeniyar

John Kerry Nigeria Afrika 25.1. James Entwistle
Ko a watan jiya 'yan takarar biyu sun gana kan wannan batu da John KerryHoto: Reuters/Akintunde Akinleye

“Mun sake taruwa a yau domin jaddada alkawarinmu na zabe a cikin zaman lafiya. Saboda haka muna kiran 'yan kasa da ragowar magoya bayan mu da su kaucewa duk wani abun dake iya jawo tashin hankali ko kuma kawo matsala ga fatanmu na samar da ingantaccen zabe. Sannan kuma muna kiran hukumar zabe da sauran jami'an tsaro da su tsaya a kan matsayin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora musu.

Kuma mun yi alkawarin mutunta sakamakon zabe mai inganci”

Akwai alamun sauyi a sabuwar yarjejeniyar

Sabuwar yarjejeniyar dai na nuna alamun sauyin yanayi a kasar da ta dauki lokaci tana taci ba taci ba game da makomar zaben dake zaman irinsa mafi zama a shekaru 16 na sake girka demakaradiya. Janar Muhammad Buhari dai zaman dan takarar dake ka neman kwace goruba a hannun kuturu,

“Mu dai Najeriya muka sa a gaba kowa yayi hakuri ya sa kuri'arsa insha Allah ba za'a samu tashin hankali ba. Da mutanen INEC da jami'an tsaro kowa yayi aikinsa akan kundin tsarin mulkin Najeriya kuma kowa ya san aikinsa akan tsarin mulkin Najeriyar”

'Yan takarar sun yi alkawarin rungumar kaddara

Duk dai da cewar babu wasu jawabi daga shi kansa shugaban da ke fuskantar yanayi maras tabbas kuma yayi nisa a karatun runguma ta kaddara in hali yayi, ko kuma shi kansa Buharin da a baya ake yiwa kallon gaza hakuri da runguma ga kaddara, a fadar Janar Abdusalami Abubakar da ke shugabantar kwamitin dai batun zaman lafiya na gaban duk wani ra'ayi

Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi
Tuni dai gwamnati ta fara tura jami'an tsaro yankunan kasarHoto: Getty Images/AFP

“Kasannan fa muna son zaman lafiya muna bukatar dan Allah don Annabi ayi zabe cikin zaman lafiya duk wanda Allah yaba to a bashi. Ba mu makara ba mun dade muna aikin tabbatar da zaman lafiya, kuma aski ne yazo gaban goshi. Ya kuma bamu alkawarin duk wanda yaci zamben nan shi zai ba mulki”

Tuni dai kallo yana shirin komawa sama cikin kasar dake tsakanin tabbatar da zaben da babu irinsa da kuma fuskantar barazanar rigingimun da babu kamarsu.