1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yanci ko ƙarfi na ga Al´umma -Ƙungiyoyin kare haƙƙin al’umma da Sabuwar Afirka

March 30, 2010
https://p.dw.com/p/DrH1
Hoto: achim Pohl/Das Fotoarchiv

‘Yanci ko Ƙarfi na ga Al’umma -Ƙungiyoyin kare haƙƙin al’umma da sabuwar Afirka.

Al’ummar nahiyar Afirka na hanƙoran ganin an samu dauwamammiyar dimokuradiyya a Afirka, tare da ganin an kawo ƙarshen rashawa da cin hanci da ya yi katutu, a kuma samu haɗin kai da juna. Hakan ne kaɗai zai kawo canjin da ake buƙata.

A shekara ta 2002, shugaban ƙasar Zambiya Frederick Chiluba, ya bayar da shawarar cire wani sashe a kundin tsarin mulkin ƙasar domin ya samu ya ci gaba da mulki a karo na uku, amma ina, jama’ar ƙasar suka fito ƙwansu da kwarkwata suka ce ba su yarda ba, wannan bore ya hana ‘yan majalisar rattaba hannu akan dokar.

Sabon Alfijir

Yanzu a ƙasashen Afirka da dama, danniya da babakeren shugabanni da aka saba yi ya zo ƙarshe. Yanzu jama’a na bin kadin haƙƙinsu ta hanyar ƙin amincewa da duk wani ƙudiri da ba su amince da shi ba, daga ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da waje

Dama ko ‘yanci na hannun Al’umma

Akwai dalilai da dama da suka sa shirin Ji ka Ƙaru yake nazari akan yadda ƙungiyoyi masu hanƙoran ‘yancin ɗan Adam a Afirka suke gudanar da ayyukansu. Ba wai yana duba ayyukan da suke yi a siyasance ba, a’a, har ma da tallafi da suke bayarwa da kuma irin ƙoƙarin da suke yi na kawo zaman lafiya da kuma shirin kauda fatara da talauci.

Shirin zai yi tattaki zuwa ƙasashen Laberia da Kenya, domin ya kawo wa masu sauraro irin faɗi tashin da ɗan Afirka yake yi don cimma burin nahiyarsa.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.