1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin siyasar Najeriya a jajibirin kama milkin Gwamnati

Gazali Abdu Tasawa/Pinado Abdu WabaMay 21, 2015

Batun gadon bashin kudade da gwamnatin Goodluck ke shirin bari ga sabuwar gwamnati dama na murabus din shugaban jamiyyar PDP na kasa Ahmed Adamu Mu'azu na daukar hankali a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1FThL
Nigeria Goodluck Jonathan Abdulsalami Abubakar Muhammadu Buhari
Hoto: DW/Ubale Musa

A cikin kundin namu na yau muna dauke da jerin rahotanni kan yanayin da siyasar Nageriya a daidai lokacin da ake shirye-shiryen mika milki ga sabuwar gwamnati.

Muna dauke da rahoto kan batun bashin kudi da gwamnatin Goodlock ke neman dauka domin biyan albashin ma'aikata, akwai kuma maganar kudadan bashi da gwamnati mai barin gado ta gada da kuma wadanda take shirin bari ga takwararta mai jiran gado.

Haka zalika akwai maganar murabus din da shugaban jamiyyar PDP na kasa ya yi daga kan mukaminsa dama mahawurar tare da sharhunan da masana kimiyar siyasa dama sauran yan Najeriya ke yi akan matakin da tasirin da zai yi akan makomar jamiyyar PDP dama a fagyen siyasar Najeriya baki daya.