1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Siriya miliyan 10 sun dogara ga tallafin abinci

July 21, 2014

Kungiyar ba da taimakon abinci a duniya da ke Jamus ta ce miliyoyin 'yan gudun hijirar Siriya na cikin hali na tagaiyara sakamakon yakin basasar kasar.

https://p.dw.com/p/1CgKf
Welthungerhilfe zu syrischen Flüchtlingen
Hoto: Welthungerhilfe

Alkalumman da kungiyar ba da taimakon abinci ta duniya ta bayar na nuna cewa halin da 'yan gudun hijirar Siriya ke ciki ya kara yin muni, inda ta ce mutane fiye da miliyan 10 sun dogara kacokan kan taimakon abinci. Jami'in da ke kula da ayyukan kungiyar a kasashen Siriya da Turkiya Ton van Zutphen ya nunar da haka a nan birnin Bonn inda ya kara da cewa yakin da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye, na janyo cikas ga kokarin kungiyoyin agaji na duniya kai agaji ga mubakata. Ya ce fadan da ake yi tsakanin su kansu kungiyoyin 'yan tawayen da ke adawa da juna na kawo babban cikas. Ya ce da yawa daga cikin ma'aikatansu ba sa iya shiga wadannan yankuna saboda rashin tsaro.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar