'Yan sanda sun buɗe wuta a kan masu bore a Burkina
October 30, 2014Talla
Tun farko masu yin boren sun ƙone ginin majalisar dokokin ƙasar a yau,a dai dai lokacin da aka shirya majalisar za ta tattauna ƙudirin bai wa shugab Blaise Compaore damar yin takara a a zaɓen shugaban ƙasar wa'adi na biyar.
Sannan kuma a garin Bobo Dioulasso, birnin na biyu mafi girma na ƙasar an ba da rahoton cewar an ƙone ofishin magajin garin birnin da kuma cibiyar jam'iyyar da ke yin mulki.