1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da bauta a duniya

Salissou IssaDecember 3, 2014

An samu canji da salo daban-daban na bautar da jama'a duk da kokarin da kasashen duniya ke yi na hana bautar da mutane.

https://p.dw.com/p/1DyfN
Protest gegen Sklaverei in Großbritannien Oktober 2013
Hoto: Getty Images/P. Macdiarmid

Ranar biyu ga watan Disemba rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da bauta, wacce ta samo asali tun a shekarar 1949. Sai dai a wannan karni na 21 akwai canji ko sabbin dubarun bautar da jama'a duk da dokokin da aka shata na hana bautar da mutane. Shin ko yaya yanayin bautar yake a jamhuriyar Nijar da ke yankin yammacin Afirka?

"Yaki da bauta kokowa ce ta kullum" shi ne jigon bikin na bana. Wannan rana ta yaki da bauta na da salsala ne daga soke bautar bayi bakake. A yanzu dai akwai sabbin salo na bautar da ke hana wa dan Adam wasu hakkoki ko 'yanci nasa da ake yi a boye. Wannan kuma ya hada aikin yara da safarar mutane da nuna wariya ga wani gungu na al'umma da keta hakkokin ma'aikata 'yan ci rani da lalata da yara kanana sannan da saka mata ko 'yan mata karuwancin tilas.

Bauta na ci-gaba a wasu sassan Nijar

Symbolbild Moderne Sklaverei Menschenhandel Ghana
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Ridley

Abubakar Fakandau na kungiyar Timidiriya da ke yaki da bauta a Nijar ya bayyana cewa har yanzu a wasu yankuna na kasar ana bautar da jama'a.

"A wasu wurare cikin daji har yanzu kana ganin bayi suna aiki. Jihar Tahoua akwai su. A Tilaberi ma akwai su cikin daji. Sun daukesu kamar dabbobi, ba su da 'yancin zuwa makaranta. Hakan nan ma suna aurar 'yan mata ba bisa hakki ba. Sun daukesu tamkar hajjarsu."

Maryama wata yarinya da ke aikin gida ta bayyana yadda uwargijinta ta azabtar da ita ta fannin sakata ayyuka ba kakkautawa tare da ba ta kashi.

"Shara da wanke-wanke da zuwa sayayya. Da hannuna nake yi mata surfe sannan ta ce in kara daka mata tsaki, ba ta kaiwa manika inji ya nika mata. A safiyar Sallah ta dauko bulala ta mare ni, da na tambayeta don me ta mare ni? Sai ta ba ni kashi. Kudina ma ba ta ba ni."

Cikakken hadin kai a matakin kawo karshen bauta

Elfenbeinküste Symbolbild Sklaverei
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Majalisar Dinkin Duniya na aiki da gwamnatoci da kungiyoyin kwadago da na farar hula a cikin kasashen duniya ta hanyar ba su horo domin gano sabbin salo na bautar da jama'a don yaki da su tare da shimfida dokoki na hukunta masu bautar da mutane. Madame Gani Salamatu ta ma'aikatar ci gaban mata da kare yara kanana a Jihar Maradi cewa ta yi.

"Akwai hukunci, tun da cikin babban kundinmu na dokoki an soke bauta. Duk dan Adam yana da 'yancin kanshi, ke nan bai kamata wani yayi sufuri da shi ba."

Burin saka kungiyoyi da kasashe da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a cikin wannan yaki da bauta, shi ne waye kan al'umma a kan barin wannan mummunar dabi'a. Sannan da hada kai don dakile fataucin mutane da karuwancin 'yan mata da mata da ake tilasta ma wannan sana'a ba da son ransu ba.

Ya zuwa yanzu babu wasu alkalumma sahihai game da yawan wadanda ake bautarwa a Nijar. Sai dai ko shakka babu yara kanana musamman 'yan mata na cikin wadanda wannan lamari na bauta ya fi shafa.