1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaduwar cutar Ebola na janyo fargaba

July 28, 2014

Hukumar kula da lafiya WHO ta ce akalla mutane 660 suka rasu sakamakon cutar amma kuma ta yi kira ga duk wanda ya ga alamu ya je asibiti domin samun daukin gaggawa

https://p.dw.com/p/1CjjZ
Ebola in Liberia
Hoto: picture-alliance/dpa

Fargaba ya karu da safiyar yau litini bayan da aka wayi gari da rasuwar mutumin farkon da ya kamu da cutar Ebola a babban birnin Saliyo wato Freetown a yayin da wani likita baamurke da wata ma'aikaciyar agaji su kuma suka kamu da cutar a Liberia, abin da ya kara adadin ma'aikatan lafiyan da suka kamu da cutar.

Kamfanin dillancin labarun AFP na Faransa, ya rawaito cewa mutanen biyu suna karbar magunguna kuma suna samun sauki, inda mahukuntan asibitin da mutanen biyu ke jinya kuma suka jaddada cewa karbar magunguna tun ciwon bai yi nisa ba ne ke tabbatar da waraka.

Alkaluman da Hukumar lafiya ta Duniya ta fitar sun nuna cewa kusan mutane 660 ne suka hallaka sakamakon wannan cuta a yankin yammacin Afirka.

Wannan cuta mai hadarin gaske kan yadu ta musayar ruwan jiki ne kamar zufa, ma'ana za a iya kamuwa da ita ko ta yin masabaha da mai dauke da cutar, kuma tunda babu magani, dole a kebe duk wanda aka gani da cutar domin rage yaduwarta

Arik Air, daya daga cikin jiragen saman da ke jigilar fasinjoji a Najeriya ya ce ya dakatar da tafiya zuwa kasashen Liberia da Saliyo kasancewar a tsakaninsu kawai cutar ta hallaka mutane 350.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu