1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda a ke tantance minista a Najeriya

July 7, 2014

Kafin shugaban kasa ya gabatar da sunayen wadanda za a tantance ga majalisa, sai ya yi la'akari da jihohin kasar 36 ya tabbatar bai karkata ga wani yanki fiye da wani ba

https://p.dw.com/p/1CXOC
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Tantance duk wanda shugaban kasa ya ke so ya ba mukamin minista, ana bin shi hawa-hawa ne. Da farko, shi kan shi shugaban kasar, zai tantance mutane ne daga cikin wadanda aka gabatar masa, ta yiwu daga 'yan jam'iyya ko kuma tsakanin wasu mutane masu fada a ji.

Daga nan ne shugaban kasa zai yi na sa dan binciken, ya duba ya gani, misali, ta fiskar siyasa wace gudunmawa ce mutumin ya bayar, kana wace irin gudunmawa shi mutumin zai bayar idan an zabe shi. Bayan wannan sai a je mataki na biyu wato tantancewar jami'an tsaro.

Su ma za su duba su gani ko wannan mutumin ya cancanta ko bai cancanta ba. Da zarar mutumin ya wuce wadannan matakai biyu, sai shugaban kasa ya tura shi ga Majalisar Dattijai.

Rawar da Majalisar Dattawa ke takawa

To amma, kafin a kai ga kiran mutumin ya zo ya amsa tambayoyi cikin Majalisar, sai su kansu, sanatocin sun gudanar da na su binciken domin su tabbatar cewa ya wuce matsalar tsaro, sa'annan sai a duba irin mukamin da yake rike da shi, misali, illimin da ya ke da shi, da cancantarsa da kwarewarsa a wannan fanin.

Sannan ne za a kai shi Majalisar Dattawan, a yi mi shi binciken kwakwap a kuma yi masa tambayoyi.

Tambayoyi iri-iri ne, su kan fara da duba cancantar mutum. Misali, idan za a yi ma mutun minista na tsaro ko na illimi, sai a duba irin illimin da ya ke da shi a wannan fanni daga sai a tambaye shi, idan har aka ba shi wani mukami misali, mene ne ya ke gani yana da shi da zai nuna ya cancanci a ba shi Minista.

Tantancewar dai ya danganci irin matsin lambar da shugaba ya ke samu daga wadanda suka gabatar da mutumin da kuma kwarewar shi.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar