1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

William Ruto ya gurfana gaban kotun ICC

September 10, 2013

Kotun ƙasa da ƙasa da ke hukunta mayan laifukan yaki wato ICC na zaman shari'ar mataimakin shugaban ƙasar Kenya William Ruto bisa laifin take yancin ɗan Adam.

https://p.dw.com/p/19eYR
Former Kenyan Education Minister William Samoei Ruto sits in the courtroom of the International Criminal Court (ICC) in The Hague, Netherlands, Thursday, Sept. 1, 2011. Ruto is one of three senior Kenyan leaders appearing at the International Criminal Court for a hearing at which judges will decide whether evidence against them is strong enough to merit putting them on trial on charges of orchestrating deadly violence in the aftermath of disputed 2007 elections. (Foto:Bas Czerwinski/AP/dapd)
Mataimakin shugab kasar Kenya, William RutoHoto: AP

Mataimakin shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya gurfana gaban kotun hukunta manyan laifuka da ke birnin Hague wato IC, bisa tuhumarsa da hannu a rikicin da ya zubar da jini bayan zaɓe ƙasar shekaru biyar da suka gabata. Shi ma dai shugaban ƙasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya na fuskantar tuhuma kan wannan rikicin bayan zaɓen inda aka sa watan Nowamba a matsayin lokacin da zai gurfana a gaban kotu.

Kenyatta da Ruto waɗanda da ke gaba da juna kafin su haɗe, ana tuhumarsu da haddasa rikici tsakanin ƙabilar Kikuyu da Kalenji, inda suka yi amfani da adduna da takkuba da mashi wajen hallaka juna. An yi ƙiyasin cewa kimanin mutane 1,200 suka mutu kana wasu dubbai suka rasa mastugunai sakamakon rikicin.

Wannan shari'ar dai wani gwaji ne ga ƙarfin kotun ta ICC, wacce ake zargin da sa ido don hunkunta 'yan asalin nahiyar Afirka, yayin da ta ke burus da sauran laifukan yaƙi wanda wasu ƙasashen masu faɗa aji a duniya ke aikatawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe