1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Watanni shida ke nan da sace 'yan matan Chibok

Uwais Abubakar IdrisOctober 16, 2014

Tun bayan kame 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta yi, har yanzu ba’a kai ga gano koda guda daya ba duk da ikirarin gwamnatin Najeriya na cewa ta san inda su ke.

https://p.dw.com/p/1DVaz
Boko Haram Video 12.5.2014
Hoto: picture alliance/abaca

To yanayi ne dai na nuna alhini takaici da ma juyayi ga mafi yawan iyaye da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace, musamman ‘yayan kungiyar Bring back our girls da suka kai ga zubar da hawaye saboda halin da babu wanda ya sani da ‘yan matan na garin Chibok ke ciki. Shiga hali na Allah babu ya Allah da wadanan ‘yan mata 219 da watani shida cur ke nan ana neman kaiwa ga kwato su amma ba tare da samun nasara ba.

Gangami, matsin lamba da ma fito na fito da 'ya'yan kungiyar Bringback our girls suka yi duka ya gaza kaiwa ga biyan bukata, abin da ya sanya Malama Hadiza Bala Usman jigo a kungiyar Bringback Our girls bayyana yadda suke ji da aka kai wannan lokaci ba tare da gano ‘yan matan ba.

‘'Wannan rashin gano yaran nan ya dame mu matuka saboda yau a ce babu labari, ko yarinya daya ba'a ceto ba. Mu abind a muke so mu nunawa duniya cewa ba zai yiwu ba a ce an mance da ‘yaya 219 har ya zu wata shida sun bace. To dole a tashi tsaye kasashen dunoya da suyka bada taimako wane sakamako wannan ya bayar''.

Nigeria Protest Boko Haram Entführung 26.5.2014
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Gwmanatin Najeriya ta ce za ta ceto 'yan matan

Kodayake gwamnatin Najeriyar na mai ikirarin cewa tafa san inda ‘yan matan suke kuma in aka bi a hankali za ta kai ga ceto su, kalaman da a kullum ke kara jefa fata a zukattan iyayen yaran da tuni fiye da bakwai daga cikinsu suka mutu saboda shiga hali na damuwa. To ko me wannan ke nunawa a bangare batun tsaro musamman gaza gano ‘yan matan na Chibo? Malam Kabiru Adamu kwarrare ne a harkar tsaro a Najeriyar.

"Ba wai maganar makarantu ba ne ai ina ganin ai in ka duba barikokin sojoji da ma wasu wurare ana kai masu hari, don haka ba yadda za'a aiwatar da wannan. Don haka ni ban yi mamaki bad a har yanzu bamu ga tasirin da aka samu a wannan shiri ba''

A yayinda 'ya'yan kungiyar Bringback our girls ke kara kaimi da gangami na nuna juyayin rashin gano ‘yan mata na garin Chibok, ga gwamnatin Najeriya wannan batu na ci gaba da zama gagarabadau ga wa'adin mulkinta musamman a dai dai lokacin da take fuskantar zabe.