1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wahalar man fetur ta yi kamari a Najeriya

Ahmed SalisuMarch 3, 2015

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewar ana ci gaba da samun karuwar karancin man fatur a kasar, lamarin da ya jawo tsaiko a harkoki na yau da kullum.

https://p.dw.com/p/1Ek7T
Benzin Afrika
Hoto: picture-alliance/ dpa

Masu aiko da rahotanni suka ce wannan matsala ta shafi manya da kananan biranen kasar, kana hakan ya sanya wasu gidajen mai musamman ma na 'yan kasuwa na sayar da man a farashin da ya zarta wanda hukumomi suka sanya.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce ta tashi haikan wajen kawar da wannan matsala cikin hanzari wadda a cewarta wasu gungu na jama'a ne suka kirkir ta sanadiyyar boye man da suka yi.

Tuni dai hukumomi suka ce za su sanya kafar wando guda da masu wannan dabi'a da ma wadanda ke amfani da wannan dama wajen sayar da man fiye da farashin da gwamnati ta sanya na Naira 87 a kan kowacce lita.