1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa'adin zaben sabon shugaban majalisa a Nijar

Mahamane KantaNovember 21, 2014

Kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar, ta ayyana cewa babu kowa a kan kujerar shugaban majalisar dokokin kasar, bayan da Shugabanta Hama Amadou ya yi gudun hijira zuwa kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/1Dr6I
Hoto: DW/M. Kanta

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan majalisun dokoki na bangaran masu rinjaye, suka shigar da kara a gaban kotun na neman ta tabbatar da rashin shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijar kan mukamin sa bayan da ya bar kasar yau kusan watanni uku kenan inda ya ke gudun hijira a kasar Faransa.

Hajiya Hauwa Abdu
Hoto: DW/Mahamman Kanta

Dangane da hakka ne ma, kotun tsarin mulkin ta nemi da majalisar dokokin kasar ta Nijar ta zabi sabon shugaba cikin kwanaki 15 masu zuwa daga lokacin da ta bayyana wannan hukunci kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Tuni dai 'yan majalisa na bangaran masu rinjaye da suka shigar da wannan kara, suka nuna gamsuwarsu da wannan hukunci, inda suka ce za su dukufa wajan zaben sabon kakakin majalisar don mutunta hukunci. Daga nasu bengare 'yan majalisar dokokin na bangaran adawa ta bakin Bakary Saidou na jam'iyar Moden Lumana Afrika ta Hama Amadu, ya ce a halin yanzu dai ba su da wani bayyani amma kuma nan ba da dadewa ba bangaran adawa na ARDR zai fitar da tashi sanarwa kan wannan batu domin bayyana nasu matsayi.

Tun daga ranar 27 ga watan Augusta da ya gabata, bayan yunkurin da hukumomin kasar suka yi na kama shi sakamakon tuhumar sa da ake da hannu cikin safarar jarirrai, Hama Amadou ya bar kasar ya zuwa kasar Faransa inda ya ke gudun hijira, sai dai tun wannan lokaci hama Amadou ke ikirarin cewa wannan wani mataki ne da gwamnati ta dauka na nuna karfin iko don hana masa tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2016, batun da hukumomin na Nijar suka karyata.

Hama Amadou
Hoto: DW/S. Boukari