1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da rufe sansanin gwale-gwale na 'yan Nazi

Ummaru AliyuJanuary 27, 2015

A Talatar nan 27 ga watan Janairu, aka cika shekaru 70 da kawo karshen sansanin gwale-gwale da aka fi sani da suna Auschwitz na 'yan Nazi.

https://p.dw.com/p/1ERHC
Konzentrationslager Auschwitz-Birkenau
Hoto: DW/D.Bryantseva

A cikin shekara ta 1941 ne aka kafa sansanin a Poland wanda shi mafi girma daga cikin dukkanin sansanonin gwale-gwale wadanda suka zama wuraren kisan Yahudawa. Sunan sansanin na Auschwitz kadai ya zama wata alama ta rashin imanin da 'yan Nazi da suka yi mulki a Jamus suka aiwatar kan Yahudawa da sauran tsiraru a nahiyar Turai kafin karshen mulkin nasu a shekara ta 1945.

Auschwitz-Birkenau Gedenkfeier am 27.01.2015
Mahalarta bikin cika shekaru 70 da rufe sansanin gwale-gale na 'yan Nazi.Hoto: Reuters/Laszlo Balogh

Daga cikin Mutane miliyan shidda da suka halaka sakamakon abin da aka sani da suna Holocaust, akalla miliyan daya da dubu 100 daga ciki har da Yahudawa miliyan daya kuma an kashe su ne a sansanin na Auschwitz ta hanyar amfani da iskar gas mai guba yayin da wasu suka mutu sakamakon wasu cutuka da rashin kula. A tsawon mulkin da 'yan Nazin suka yi tsakanin shekara ta 1933 zuwa shekara ta 1945, sun rika kwashw jama'a musaman Yahudawa zuwa sansanonin gwale-gwale da suka kafa a kasar ta Poland da suka mamaye.

Daya daga cikin mutanen da suka tsira da rayukansu daga sansanin na Auschwitz, Esther Bejarano 'yar shekaru 90 da haihuwa, ta tuna rashin imanin da ta gani a sansanin na Auschwitz musamman daga likitan sansanin watao Dr. Mengele. Inda ta ke cewa ''idan ya zo gabanmu ya kan nuna alama da hannunsa ya nuna hagu ko dama. Idan ya nuna alamar hagu to wanda aka nuna ya na da dan sauran lokaci kafin rayuwarsa ta kare. Idan kuwa ya nuna dama to wanda aka nunawa nan take a kan wuce da shi dakin da za a kashe shi da gas mai guba.

Baya ga Yahudawa da suka hallaka, 'yan Nazi din sun kashe 'yan kasar Poland da tsirarun kabilu kamar Sinti da Roma a sansanin. Ko da shi ke 'yan Nazin sun bude wasu sansanoni inda suka rika kashe jama'a, kamar wadanda ke Majdnek da Treblinka da Ravensbrueck ko Dachau da Buchenwald amma sansani mafi girma dake Auschwitz sai ya zama alama ta munin rashin imani da kisan jama'a a sansanonin gaba dayansu.

Auschwitz-Birkenau Gedenkfeier am 27.01.2015
Roman Kent na daga cikin wanda suka tsira daga sansanin gwale-gale na 'yan Nazi.Hoto: Reuters/Laszlo Balogh

A yau, biyu daga cikin sansanonin na gwale-gwale na 'yan Nazi ciki har da na Auschwitz har yanzu suna nan kuma mafi yawan kayan da akai amfani da su domin halaka jama'a suna nan a matsayin kayan tarihi, inda ma wadannan sansanoni suka zama wani bangare na gidan tarihin Aschwitz Birkenau. Burin hakan dai shi ne fadakarwa da tunatar da zuriyar Jamusawa da aka haife su bayan yakin duniya na biyu game da rashin imanin da 'yan Nazi suka aikata musamman kan Yahudawa.