1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da fara yakin duniya na biyu

September 1, 2014

Shugabannin Jamus da Poland za su yi alhinin da fara yakin duniya na biyu shekaru 75 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/1D4fh
Hoto: picture-alliance/akg

A wannan Litinin ake bukukuwan tunawa da cika shekaru 75 da fara yakin duniya na biyu. Shugaban Jamus Joachim Gauck zai hadu da takwaransa na kasar Poland Bronislaw Komorowski a mashigin ruwan Gidansk. Shugabannin biyu za su kunna wutar candle a kan makabartar sojojin da suka kwanta dama.

Yakin duniya na biyu ya fara da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Satumban shekarar 1939 lokacin da dakarun ruwan kasar Jamus suka bude wuta kan Poland a wannan mashigin ruwan. Kafin wannan lokaci 'yan Nazi na Jamus sun kirkoro yanayi da ke nuna cewa Poland tana yi wa Jamus kutse. Wannan hari da dakarun Jamus karkashin gwamnatin Nazi da Adolf Hitler ke jagoranta, ya janyo kasashen Birtaniya da Faransa suka kaddamar da yaki kan Jamus ranar 3 ga watan na Satumban.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal