1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaiko na zirga-zirga a Najeriya saboda matsalar man fetur

Mansur Bala BelloMarch 5, 2015

Birnin Lagas na ɗaya daga cikin biranen ƙasar da ya tsunduma cikin wannan matsala.

https://p.dw.com/p/1ElPF
Verkehrsstau in Lagos Nigieria
Cinkoson motoci a LagasHoto: AP

Matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a najeriya ta janyo tsaiko a kan harkoki na zirga zirga a kasar.Misali a Lagas lamarin ya haddasa tafiyar hawaniya ga sha'anin zirga-zirgar kana kuma frashin sufiri ya hau wanda jama' suke ta yin kuka da rashin man.

Matsalar ta haddasa hauhawar frashin sufiri

Cinkoson motoci a Lagas
Cinkoson motoci a LagasHoto: AP

A koina a kan tittuna a birnin na Lagas jama'a sun ja dogayen layuka a gidajen mai, sannan kuma mutane na zube barjat kan hanya suna jiran motocin haya na shiga. Waɗanda saboda wannan hali da aka samu kai a ciki frashin sufirin za ƙaru.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani