1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta tsakanin Boko Haram da gwamnatin

Usman Shehu UsmanOctober 18, 2014

A daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar cewa ta cimma yarjejniyar tsagaita bude wuta da Boko Haram, Kungiyar ba ta kai ga tabbatar da matsayin kan lamarin ba.

https://p.dw.com/p/1DX7a
Nigeria - 54. Unabhängigkeitstag
Hoto: DW/U. Musa

Labarin cimma yarjejeniyar dai na zuwa ne dai dai lokacin da shugaban Najeriya ke daf da bayyana matsayinsa a sake tsayawa takaran zaben badi.

Rahotanni da suka fito daga bakin jami'an gwamnatin Najeriya, sun suka ce wai ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Kungiyar Boko Haram da batun sako yaran nan 'yan makarantar Chibok sama da dari biyu da kungiyar mayaƙan na Boko Haram ta sace sama da watanni shida.

Sai dai fa wadannan bayanan sun fito ne daga wasu majiyoyi na fadar shugaban ƙasa. Inda suka ce ya zuwa yanzu batutuwa biyu aka cimma ƙarƙashin wannan yarjejeniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya shaidar, sune ɓangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta sannan za a sako yaran nan na Chibok da aka kama a makarantarsu da ke a arewa maso gabashin Najeriya.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Yaran 'yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali a BamaHoto: Reuters/S.Ini

Halinda ake ciki a yankunan Boko Haram

Bayanai na baya sun nunar da cewa jami'an tsaron Najeriya sun kwato wasu daga cikin garuruwan da ‘yan Kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ta karbi ikonsu tun a watan Agusta da ya gabata. Sai dai sabobbin bayanan da ke fitowa daga wadannan yankunan na tabbatar da cewa har yanzu ‘yan Kungiyar na shawagi da makamansu don tsare wadannan wurare. Ko da su ma Jama'ar yankun Arewa maso gabashin Najeriya da aka ayyana garuruwansu a matsayin daular musuluci sun tabbatar da wannan labari.

Ita ma majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa wuraren nan fa har yanzu na karkashin ikon ‘yan bindigar bisa rahotanni da suka samu ta hannun ‘yan majalisar da suka fito daga wadannan yankunan. Wannan ya sa majalisar wakilan amince da wani kudiri da ke bukatar gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye, ta hanyar kara yawan dakaru da kayan yaki domin kwato garuruwan domin al'ummomi su koma wurarensu.

Yanzu haka kuma ‘yan gudun hijirar da suka fito daga Borno suna nan cikin mawuyacin hali, da ta kai yara na mutuwa saboda azabar da suke ciki inda suke neman taimako daga kowa da kowa saboda samun sauki. Masharhanta dai na bayyana damuwa kan halin da ake ciki musamman ganin al'ummar wannan yankin na Arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da fuskantar barazana na hare-hare, duk da dokar ta bacin da sama da shekara guda kenan ana aiwatar da ita.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kananan hukumomin Ngala da Kala-Balge da Bama da Gowza da Dikwa a jihar Borno da kuma wasu kananan hukumomin a jihohin Adamawa da Yobe sun fada hannun ‘yan Kungiyar da aka fi sani da Boko Haram tun watan Agusta inda suka ayyana daular musulunci a yankunan.