1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaitaccen tarihin kwammanda Sani Suna Sido

November 7, 2013

Tsohon mataimakin shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar wanda aka kashe a shekarun 1977 bayan da aka zarge shi da yunƙurin juyin mulki.

https://p.dw.com/p/1ADqL
Niger eng

An haifi kwammanda Sani Souna Sido a shekarun 1933 a Garin Libore dake da ratan kilimota biyar daga birnin Yamai mahaifinsa bazabarme ne, mahaifiyarsa ko ta garin Maradi ce da ke a yankin gabashin Jamhuriyar Nijar.Bayan ya kammala karantunsa ya shiga aikin soji a ƙarƙashin tuttar ƙasar Faransa wanda ya yi yaƙi China da na Aljeriya. A ƙarshen yaƙi bayan ficewar Faransa daga nahiyar Afirka ya kasance sojin Nijar inda ya riƙe muƙamin babban dogari na tsohon shugaban gwamnatin farar hula na farko Djori Hamani.Sannan bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙarƙashin jagorancin Janar Seyni Kuntche a shekarun 1974 kwammanda Sani Suna Sido ya zama mataimakin shugaban ƙasar.

Ya kuma fara sami matsala ne a farkon shekarun 1975 bayan da shugaban ƙasar na wannan lokaci ya tura shi Faransa domin ya tattauna da hukumomin ƙasar a kan frashin ƙarfen uranium wanda a kan haka ya yi sa' in sa' da Faransawa. Kuma bayan daworsa gida Nijar an zarge shi da yunƙurin kifar da gwamnati abin da ya sa aka kama shi aka kuma kashe shi a shekaru 1977. Sani Suna Sido dai ya taka muhimmiyar rawa a cikin yaƙin Biafra wanda ya ba da goyon baya ga yan arewa.

Daga ƙasa za a iya sauraron shirin namu baki ɗayansa domin jin ƙarin baiyani

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba