1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habakar tattalin arzikin Ghana

January 21, 2015

A nahiyar Afirka Ghana na daga cikin kasashen da ke kula da demokradiyyarsu ta yadda take tasiri a tattalin arzikin kasa tana kuma habaka kasuwanci.

https://p.dw.com/p/1ENoI
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Shaidar da 'yan kasuwar Jamus da ke zuba jari a Gahanan suka yi mata ke nan a yayin da suke ganawa da takwarorinsu na Ghanan da suka kawo ziyara nan Jamus karkashin jagorancin shugaban kasa John Dramani Mahama. Bankin KFW wanda ya shahara wajen zuba jari domin inganta tattalin arzikin kasashe tare da tallafin kungiyar kawancen kasuwanci a tsakanin Afirka da Jamus ne suka shirya wannan taron, inda suka gayyaci shugaban kasar Ghana tare da manyan 'yan kasuwa su yi musu bajekolin irin fannonin da ya kamata su dada zuba jari.

Gasag-Summer School 2011
Hoto: DeCo!-Sustainable Farming

Dalilan zuba jari a Ghana

Daya daga cikin shugabanin bankin na KFW Mr Bruno Wenn ya yi mana karin haske dangane da dalilin da ya sa tauraruwar Ghanar ke haskakawa a idanunsu

"A ra'ayin 'yan kasuwar Jamus Ghana tana da dama da suke daga mata kima, na farko suna amfani da harshen Ingilishi wanda ya fi sauki ga Bajamushe akwai saukin zuwa, kuma akwai daidaito a fanin demokradiyya da tattalin arziki idan aka yi la'akari da shekaru 10 da suka gabata"

Kasim Halidu Ahmed jami'i ne a kamfanin Olam Ghana kamfanin da ke sayen amfanin gona daga kananan manoma yana sarrafawa kana a fitar da su zuwa kasashen da ake bukata, ya ce suna ma kokarin fadada aiyukansu a dalilin dangantakarsu da Jamus.

Kamfanin Siemens na daya daga cikin manyan kamfanonin Jamus da ke alfahari da dangantakarsu da Ghana musamman a fanin makamashi kamar yadda shugabar kamfanin, reshen Ghana Sabine Dall'Omo ta bayyana

Gasag-Summer School 2011
Hoto: DeCo!-Sustainable Farming

Me ke jan hankalin 'yan kasuwar?

"Makamashi ya ja mana hankali sosai a Ghana saboda irin nauo'in da suke bukata, domin tana bukatar na gargajiya da aka saba da kuma irin wadanda ake sabuntawa kuma muna da kwarewa a kan dukan su."

Shugaban kasar Ghana John Mahama wanda ya jaddada mahimmancin dangantakar kasarsa da Jamus ya kuma ce akwai yunkurin da ake yi domin inganta dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka. 'Yan kasuwar Jamus din dai na kallon Ghana a matsayin wata kofa ta shiga kasuwannin yankin yammacin Afirka.