1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin hukumar zaben Najeriya ta INEC

Ahmed SalisuJanuary 5, 2015

A shekara ta 1998 ne dai aka kafa INEC karkashin jagorancin shugaban mulkin sojan Najeriya Najeriya na wancan lokacin Janar Abdulsalami Alhaji Abubukar.

https://p.dw.com/p/1EF7z
Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Hoto: AP

Ita dai wannan hukuma ta INEC an nauyin shiryawa da gudanar da zabuka a kasar baki daya. To sai dai kafin wannan hukama, an kafa wasu makantanta a lokuta daban-daban don gudanar da sabgogi na zabe da abubuwan da suka danganci hakan. Bisa ga dokar da ta kafa hukumar, an samar da hukumomin zabe wanda ke karkashin ikonta a jihohi 36 na Najeriya wadda babban jami'i ke jagoranta da kuma sauran ma'aikata da ke dafa masa wajen gudanr aiyyukan hukumar a ofishin.

Afrika Wahl in Mali 15.12.2013
Hoto: AFP/Getty Images

Ita dai wannan hukuma ta INEC ta fara karya kummalo ne da gudanar da zabukan shekara ta1999 da ya samar da gwamnatin da shugaba Olusegun Obasanjo ya jagoranta bayan da soji karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubukar suka mika mulki ga hannun farar hula.

Mai shari'a Ephraim Akpata ne mutum na farko da ya jagoranci hukumar kuma ya fuskanci kalubale da dama bayan zaben na farko da ya shirya musamman ma dai ta fuskar rashin inganci zaben wanda ya san 'yan kasar da masu sanya idanu sukar yadda lamura suka wakana a wancan lokacin to sai dai hukumar ta musanta batu na magudin zabe.

Sauran matanen da suka jagoranci wannan hukuma baya ga Ephraim Akpata da ya rasu a shekara ta 2000 sun hada da Abel Gubadiya tsakanin shekarar ta 2000 zuwa 2005 sai Maurice Iwu tsakanin 2005 zuwa 2010 wanda a zamaninsa ya ce hukumar ta haramtawa masu sanya idanu na zabe daga kasashen waje shiga kasar don duba gudanar zabuka na 2007, matakin da aka yi Allah wadai da shi. Sai kuma Farfesa Attahiru Jega da ya aka nada a masatyin shugaba daga 2010 zuwa yau. Ita dai hukumar zaben ta INEC ta shirya zabukan da suka da na 1999 da 2003 da 2007 gami da wanda aka yi a shekara ta 2011 sannan ita ce za ta gudanar da wanda za a yi cikin watan Fabrairu na wannan shekara ta 2015 da muke ciki.

Wahlen in Mali 2013
Hoto: picture-alliance/dpa