1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin garin Minna-Najeriya

June 16, 2014

An girka garin na Minna ne da ke a cikin jihar Niger ta Najeriya a lokacin da ake yin aikin hanyar jirgin ƙasa a Najeriya, garin ya ƙunshi Hausawa, Fulani, Nufawa da sauran ƙabilu.

https://p.dw.com/p/1CJ7F
Shirin Amsoshin takardunku

Garin Minna wanda ke a yankin kudu ma so gabashin Najeriya ya samu bunƙasa ne sakamakon hulɗa ta kasuwanci da yankin ya samu tun a shekaru 1908. Shaibu Shehu Ancau wani jami'in kula da tsare-tsare na gidan tarihi na ƙasar Daura ya shaida mana cewar garin yana da cikakken tarihi tun lokacin zuwan turawan mulkin mallaka daga Ingila.

Daga ƙasa ya a iya sauraron shirin domin jin ƙarin baiyani.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu