1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihi firaministan Girka Alexis Tsipras

Ahmed SalisuFebruary 2, 2015

An haifi Alexis Tsipras a ranar 28 ga watan Juli na shekara ta 1974 a birnin Athens da ke zaman babban birnin kasar Girka kuma a ita kasar ta Girka ce ya gudanar da karatunsa.

https://p.dw.com/p/1EUMB
Alexis Tsipras Treffen mit Journalisten 24.01.2015 Athen
Hoto: Reuters/Alkis Konstantinidis

Alexis Tsipras dai ya fara harkoki na siyasa musamman ma gurguzu tun zamanin da ya ke karatunsa na sakandare don a wannan lokacin ma ya na daga cikin daliban da suka yi gwagwarmaya wajen ganin an jingine wata doka da aka fito da ita kan harkokin ilimi wadda suke dauka a matsayin illa babba ga dalibai.

Bayan da ya kammala karatunsa na sakandare, Firaminista Tsipiras ya yi aiki a kamfanoni daban-daban a matsayinsa na injiniya na gine-gine sannan a share guda ya yi rubuce-rubuce kan fagen da ya yi fice din wato harkokin gine-gine. Daga bisani kuma sai ya ajiye wannan aiki ya shiga harkokin siyasar kasar tasa ta Girka gadan-gadan.

Griechenland Wahlen 2015 Jubel bei Syriza Alexis Tsipras
Alexis Tsipras yayin da ya ke neman zabeHoto: Reuters/A.Konstantinidis

Tsipras dai na daga cikin matasan Girka da suka kasance mambobi na reshen matasa na jam'iyyar nan ta Kwamunisanci a kasar ta Girka wadda a wancan lokacin ta samu magoya baya da yawa. Sai dai daga bisani jam'iyyar ta fice daga wata gamayya ta masu tsaurin ra'ayi na sauyi amma shi Tsipras din ya cigaba da zama a cikin gamayyar har tsakanin 1999 da 2003 aka zabe shi a matsayin sakataren harkokin siyasa na reshen matasa, kana daga bisani ya rike wasu mukaman a ita wanann gamayya da ake kira Synaspismos.

A shekara ta 2006 ne ya yi takara ta majalisar birnin Athens a karkashin tutar jam'iyyar Syriza. Daga bisani kuma a shekara ta 2008 aka zabe shi shugaban Synaspismos da ke rajin sauyi, inda ya kasance shugaba mafi kankantar shekaru da ya taba rike wannan mukami don a lokacin shekarun nasa ba su wuce 33 ba. Wanann matsayi da ya rike na daga ciki irin abubuwan da suka kara sanyawa ya yi fice a kasar da ma nahiyar Turai baki daya.

A cikin shekara ta 2009 ne kuma Alexis Tspiras ya yi takara ta majalisar dokokin kasar ta Girka da ake kira Hellenic Parlament inda ya samu nasara har ma ya kai ga zama shugaban 'yan majalisa na jam'iyyar Syriza da ke adawa a majalisar. Yayin zamansa a majalisar ya yi kokari wajen ganin lamura sun sauya musamman ma dai dangane da irin halin da kasarsa ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

Alexis Tsipras ya kasance firaministan Girka bayan da jam'iyyarsa ta Syriza ta samu nasara a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a makon da a gabata. Gabannin samun nasarar da suka yi a zaben dai, jami'yyar ta Syriza ta yi ta kokarin ganin an yafe ko sake fasalta bashin da ake bin Girka in ba haka ba za su fice daga kungiyar kasashen da ke amfani da kudin bai daya na Euro wanda ake kira Eurozone.

Tsipras Vereidigung als neuer Premierminister 26.01.2015 Athen
Alexis Tsipras yayin da ya ke sanya hannu kan takardar karba ragamar mulkiHoto: AFP/Getty Images/A. Messinis

Sabon firaministan Girka Tsipras da yanzu haka ke da shekaru 40 na haihuwa shi ne firaminista mafi kankantar shekaru da kasar samu a shekaru 150 da suka gabata. Yanzu haka dai ya na da yara biyu maza wadda ya samu da abokiyar zamansa Peristera Batziana wadda suka hadu a shekara ta 1987 tun zamanin da ya ke karatun sakandare.