1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tahirin zababben shugaban Najeriya

Suleiman BabayoApril 8, 2015

An haifi Janar Mohammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar 1942, yayin da yake aikin soji dai ya rike mukaman kwamandojin soji da dama, kafin daga bisani ya zama gwamnan lardin arewa maso gabacin Najeriya,

https://p.dw.com/p/1F47b
Mohammadu Buhari
Hoto: Ekpei/AFP/Getty Images

Janar Buhari ya zama shugaban kasa a zamanin mulkin soji daga ranar 31, ga watan Disambar 1983, zuwa 27th ga watan Agustar 1985, inda a wancan lokaci ne Buhari ya kafa asusun nan na rarar mai da jama'a ke alfahari kai.

Domin kudirin samun daidaito cikin lamurar kasa nema ya sanya Janar Buhari neman shugabancin kasar a fagen mulkin demukurdiyya har sau uku, inda ya nemi shugabancin a shekarun 2003, da 2007, da kuma 2011, to amma Allah bai sa y ayi nasara ba. To sai dai a watan Disambar 2014, Janar Buhari ya sami tikitin neman shugabancin kasar karo na 4, a tutar jam'iyyar APC.

Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Presse
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis


To sai da kuma Janar Buhari ya ce shi ba kudi ne da shi ba, domin haka nema bashi da karfin aljihun da zai gudanar da kamfe na neman shugabancin kasa, dalili ke nan ma ya bude asusun da yan Najeriya ne su kansu ke yin karo-karo.

Janar Buhari ya kafa tarihi a Najeriya inda ya zama dan adawa na farko da ya kayar da jam'iyyar mai mulki, wajen lashe zaben ranar 28 ga watan Maris, inda ya kayar da Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP. Buhari yana da mata da yara 9.

Nigeria Abuja Mohammadu Buhari Anhänger Jubel
Hoto: Reuters/G. Tomasevic