1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji Burkina sun samu ministoci da dama

November 24, 2014

Firaminista Isaac Zida ya danka wa sojojin Burkina Faso mukaman ministoci masu yawa a sabuwar gwamnati da za ta jagoranci kasar na tsahon shekara .

https://p.dw.com/p/1Ds09
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabannin gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso sun amince da sabuwar majalisar zartaswa mai mabobi 25 da za ta jagoranci zabukan kasar da ma mika mulki ga hannu farar hula. Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan rantsar da sabon shugaban kasar na rikon kwarya Michel Kafando a hukumance.

A Rahotanni sun nunar da cewa an danka wa sojojin kasar mukaman ministoci masu yawa a sabuwar majalisar da za ta jagoranci kasar na tsahon shekara guda. Yanzu dai Kafando bayan mukaminsa na shugaban kasa zai kuma rike mukamin minsitan harkokin kasashen ketare, yayin da firaminstan rikon kwaryar kasar kuma wanda ya karbi mulki a hannu tsohon shugaban kasa Blaise Compaore wato Laftanar Kanal Isaac Yacouba Zida zai kasance yana rikon mukamin minstan tsaro.

Haka nan ma an baiwa jami'an sojan mukamin ministocin wasanni da na makamashi tare kuma da nada su mukaman gwanonin wasu yankunan kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Awal Balarabe