Siriya ta kori jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasarta
February 27, 2015Talla
Gwamnatin ƙasar Syria ta kori wasu jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya uku daga ƙasarta a dai lokacin da mai shiga tsakani na majalisar t ke daf da ziyartar ƙasar don tattauna yiwuwar Syriyar ta tsagaita kai hare-hare kan birnin Aleppo. Wannan matakin ana ganin zai kawo tarnaƙi ga samar da tallafi a ƙasar, a lokacin kuma da ake kan buƙatar haka.
Ana dai saran ziyarar ta Staffan de Mistura mai shiga tsakanin na MDD a gobe Asabar za ta yi tasiri ga buƙatar tsagaita kai hare-hare kan Aleppo da ke arewacin ƙasar na makonni shida.