Shugabannin Najeriya na yanzu da na jiya
Shugabanni 15 Najeriya ta yi tun bayan samun 'yancin kai a shekarar 1960 Karkashin mulkin farar hula da na soji. Mun yi muku tanadin hotunan shugabannin da irin rawar da suka taka wajen ci-gaban kasar kawo yanzu.
Janar Buhari: Zababben shugaban kasa
Zababben shugaban Kasar Najeriya na 16 bayan da ya lashe zaben da aka gudanar ranar 28 ga watan maris shekarar 2015. Zaben da aka kwatanta a matsayin mafi sahihanci a tarihin kasar, kuma shi ne shugaba na biyu da bayan mulkin soja ya zama shugaban mulkin farar hula, baya ga Obasanjo.
Firimiya Sir Abubakar Tafawa Balewa
Firaministan Jamhuriyar farko tsakanin 1 ga watan October 1960 – 15 ga watan Janairu 1966. Zaben Sir Tafawa Balewa a matsayin firaministan farko na Najeriya ya budewa kasar hanyar samun mulkin kai. A wannan lokacin dai kimar Najeriya ta daga sosai a idanun duniya saboda fafutukan da shi da sauran takwarorinsa na bangarorin kasar suka yi.
Dr Nnamdi Azikiwe: shugaba na farko
Shi ne ya kasance shugaban kasa na farko a karkashin tsarin da ya ta’allaka kan majalisar dokoki, wanda Najeriya ta yi amfani da shi daga 1 ga watan Oktoba zuwa 15 ga watan Janairun shekara ta 1966. Zik kamar yadda ake kiransa ya kasance shugaban kasa yayin da Tafawa Balewa ke firaminista kafin sojoji su yi juyin mulki.
Manjo-Janar Johnson Aguiyi-Ironsi
Ironsi ne ya kasance shugaban mulkin soji na farko a Najeriya, kuma bai dade a kan kujerar mulkin ba, hasali ma watanni shidda kacal ya yi ya na jagoranci kafin takwarorinsa sojoji da ke adawa da salon mulkinsa na amfani da tsarin da gwamnati ta fi karfi a tsakiya su yi masa juyin mulki.
Janar Yakubu Gowon
Bayan juyin mulkin ne aka dora Yakubu Gowon wanda ya kasance shugaba mafi karancin shekaru kuma shi ne ya fara kasancewa kan gadon mulki tsawon shekaru 8. Gowon ya tsara shirye-shirye da dama dan hada kan ‘yan kasa domin kawar da radadin yakin basasar da ya taimaka wajen kawo karshenshi.
Janar Murtala Ramat Mohammed
Dadewar da Gowon ya yi ya kan gadon mulki na daga cikin dalilan da suka janyo yi masa juyin mulki, wanda kuma ya sanya Janar Murtala Ramat Muhammad ya zama shugaban kasa daga 29 ga watan Yuli 1975. To sai dai bai jima ba kan mulki aka yi masa kisan gilla ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976.
Manjo-Janar Olusegun Obasanjo
Obasanjo wanda ya kasance mataimakin Murtala kafin a hallakashi, bayan da ya rasu shi ne ya karbi mulkin kasar daga shekara ta 1976 zuwa 1979. A shekarar ta 1979 ne kuma ya mika mulki ga hannun farar hula wanda a iya cewa hakan shi ne ya haifar da jamhuriya ta biyu.
Alhaji Shehu Shagari
Shehu Shagari wanda shi ne na farko daga hagu, shi ne ya karbi mulki daga hannun soji. Gwamnatinsa ta sha suka musamman daga sojin kasar kan zargi na cin hanci da rashawa da ya yi katutu a kasar. Wannan ya sanya sojin karkashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari suka yi masa juyin mulki.
Manjo-Janar Muhammadu Buhari
Gwamnatin da Janar Buhari ya girka daga 1983 ta yi aiki wajen kawar da cin hanci da rashawa a kNajeriya da ma maido da doka da oda, guda daga cikin irin shirye-shiryen da suka yi fice a gwamnatin ta Buhari shi ne shirin na WAI da ke yaki da rashin da'a. Gwamnattin Buhari ta sha zarge-zarge na keta hakkin bani Adama. Shi ma dai Buhari ya bar mulki ne ta hanyar juyin mulki a shekarar 1985.
Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Babangida ma kamar Gowon ya juma kan gadon mulki don ya jagoranci kasar ne daga ranar 27 ga watan Agustan 1985 - zuwa 26 Agustan shekarar 1993. A zamaninsa ya saurari kiraye-kirayen fararen hula na basu mulki wanda ya amince da shi amma bayan zaben da ake zaton MKO Abiola ya lashe, Babangida ya soke zaben kana ya mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya abin da ya rikita zaman lafiyar kasar.
Ernest Shonekan
Gwamnatin rikon kwaryar da Cif Ernest Shonekan (na tsakiya a hoton sama) ya jagoranta, ita ce gwamnatin mai mafi karanci wa'adi a gadon mulki. Shonekan dai ya kasance kan mulki ne daga ranar 26 ga watan Agusta na 1993 – zuwa 7 ga watan Nuwamba na wannan shekarar kafin soji su hambarar da shi.
Janar Sani Abacha
Janar Sani Abacha ne ya hau mulki bayan yunkurin da aka yi na mayar da iko a hannun fararen hula. Da dama na kallon Abacha a mastayin dan kama karya duba da irin mutanen da ya tsare har ma wasunsu suka rasu. Abacha ya yi kokari na ajiye kakin soja don jagorantar kasar a matsayin farar hula amma hakan bai tabbata ba don kuwa Allah ya yi masa rasuwa ranar 8 ga watan Yuni na shekara ta 1998.
Janar Abdulsalami Abubakar
Abdulsalami Abubakar shi ne ya kasance shugaba bayan rasuwar Abacha, inda ya kasance kan kujerar mulkin daga 8 ga watan Yuni na 1998 zuwa 29 ga watan Mayu na 1999 lokacin da Najeriya ta sake komawa kan tafarkin dimokradiyya. A wannan lokacin ne tsohon shugaba na mulkin soji Olusegun Obasanjo da bai jima da fitowa daga kurkuku ba ya zama shugaba karakshin tutar jam'iyyar PDP.
Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya yi mulki na shekaru takwas cif-cif wato daga 29 ga watan Mayu na 1999 zuwa 29 ga watan Mayun 2007. Ana yawan danganta abubuwa da dama na bunkasar tattalin arziki a karkashin mulkinsa, kuma fararen hula sun yi alfaharin kawo karshen mulkin soji.
Umaru Musa 'Yar Adua
'Yar Adua ya amshi mulki daga hannun Obasanjo, sai dai duk da irin kyakkyawar nufin da ya ke da shi ga kasar, rashin lafiya ba ta kyaleshi ya yi aiki ba. Ya yi mulki daga 29 ga watan Mayu na 2007 zuwa 5 ga watan Mayu na 2010. 'Yar Adua ya rasu kan kujerar mulki ya na da shekaru 59.
Goodluck Jonathan
Rasuwar Umaru Musa 'Yar Adua ce ta sanya mataimakinsa Goodkluck Jonathan a wancan lokacin ya ci gaba da jagorantar kasar har ma ya kammala wa'adin da suka fara tare kana ya sake yi wani wa'adin na kashin kansa kuma yanzu ma ya nemi wani karin wa'adin, amma bai yi nasara ba. Kalubalen tsaro musamman rikicin Boko Haram a zamaninsa na daga cikin abubuwan da suka fi tsaya a zukatan jama'a.