1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na shirin tinkarar zaɓuɓɓuka

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 27, 2015

Al'ummar Najeriya za su kada ƙuri'unsu a zabukan shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin ƙasar.

https://p.dw.com/p/1Eyjl
'Yan sanda na gadin katinan zabe gabanin zabukan Najeriya
'Yan sanda na gadin katinan zabe gabanin zabukan NajeriyaHoto: Plaucheur/AFP/Getty Images

'Yan takara biyu ne dai ke kan gaba wajen neman shugabacin ƙasar da suka haɗa da shugaba mai ci yanzu Goodluck Jonathan da ke takara a ƙarƙashin jam'iyya mai mulki ta PDP da kuma tsohon shugaban mulkin sojan ƙasar a ƙarƙashin babbar jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari. Zaɓen wanda tun da fari aka shirya gudanar da shi a watan Fabarairun da ya gabata, an dage shi zuwa makwanni shida wanda ya kama Asabar 28 ga wannan wata na Maris da muke ciki bisa dalilai na tsaro.