1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin barin gado a bengororin doka da na zartarwa.

Ubale MusaMay 27, 2015

Ana shirin share makon karshe ga bangarorin zartarwa da na dokar kasa cikin halin kunci da matsi, a bangaren gwamnatin da ta nuna alamar gazawa a fannoni da dama a Najeriya.

https://p.dw.com/p/1FXQI
Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz
Hoto: DW/U. Musa

To sai dai kuma ana shirin kare makon tare da gwamnatin ta Abuja da ke ci gaba da kokarin tabbatar da tasirinta cikin kasar. Duk da cewar dai sun kai ga taronsu na karshe a matsayin majalisar zartarwar lamuran kasar ta Najeriya dai , shugaban da ke shirin barin gadon yai kemudugus ga batun rushe majalisar da ta dauki shekara da shekaru tana cin karenta ba babbaka da kuma ke da ruwa da tsaki da batun asara ko nasara ta gwamnatin mai shudewa.

Alhaji Adamu MUaazu wird neuer PDP Präsident
Hoto: DW/U.Musa

Gwamnati mai barin gado na begen kujerunta

Shugaba Jonathan da mukarabbansa da ke shirin zama tarihi ya zuwa karshen makon dai, sun zabi taron na karshe wajen yaba kawunansu ga irin abun da suke yi wa kallon cigaban da gwamnatin mai shudewa ta yi nasarar samarwa ga yan kasar a shekarunta biyar na jagoranci, maimakon adabon mulki dama kila rusa ita kanta majalisar da aka zata tun da farkon fari. Kamun daga baya ya rattaba hannu kan wasu sabbabin dokoki har guda shida duk dai da nufin tabbatar da karfin ikon nasa cikin kasar har ya zuwa yanzu.

Taron karshe na majalisun dokokin kasa.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Can ma a zaurukan majalisun biyu dai wunin yau na zaman na kokarin dorawa a cikin aiyyukan da Jonathan din ke shirin bari a gadon gado ga yan kasar, inda a ranar ta yau dai shugaban ya mika bukatar neman majalisar amincewa da shawarwarin da ke kunshe cikin taro na kasar da ya kai ga gudanarwa a karon farko tun bayan komowar mulkin na demokaradiya, da kuma daga dukkan alamu yake tsoron yiwuwar sharesun a bangaren yan sauyin da ke takama da tsintsiya cikin kasar. To sai dai koma wane irin tasirin bangarorin biyu ke fatan yi a ragowar dan lokacin da ke akwai, daga dukkan alamu hankalin mafi yawan yan kasar zai koma ne a wajen dogon tarihin rashin tsaro da rushewar tattalin arziki wajen tuna sunan malafar dama masu rufa mata baya a cikin mulkin nata.