1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 50 da samun mulkin kai a Zambiya

Ummaru AliyuOctober 24, 2014

Kasar Zambiya ta cika shekaru hamsin da samin 'yancin cin gashin kai bayan da ta shafe tsawon lokaci karkashin ikon turawan mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/1DbpF
Präsident von Sambia Michael Chilufya Sata
Hoto: picture-alliance/dpa

Al'ummar kasar dai na ta nuna farin cikinsu saboda wannan lokaci da kasar ta kwashe karkashin mulkin kai. Moses Mwale da ke zaman guda daga cikin 'yan kasar ya ce murnar da suke ba za ta musaltu ba. Kwanciyar hankalin da kasar ke da shi na daga cikin abubuwan da 'yan kasar alfahari da shi musamman in aka yi la'akari da irin hali na tashin hankali da makotanta ke fuskanta a wannan lokacin.

Shugaba Kenneth Kaunda dai shi ne mutum na farko da a fara jan ragamar kasar inda ya yi mulki karkashin tsarin dimokradiyya sai dai babu jam'iyyu siyasa barkatai don a lokacin jam'iyya daya tilo ce ake da ita a kasar kuma sai da ta yi shekaru 27 da bakwai ta na mulki, to sai dai daga shekara ta 1991 aka fara aiwatar da sauye-sauye inda aka samu jam'iyyun siyasa da dama.

Masana irinsu Helmut Elischer na cibiyar Fridrich Ebert da ke birnin Lusaka na kasar ta Zambiya ya ce shekaru goma bayan gyare-gyaren da aka yi Frederick Chiluba ya so yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, yadda zai sami damar yin tazarce, kamar yadda aka saba gani a nahiyar Afirka amma nan da nan wani hadin gwiwa na kungiyoyin farar hula suka hana shi yin haka. Canji mai muhimmanci karo na uku ya samu ne a shekara ta 2011, lokacin da mulki ya koma hannun Michael Sata da jam'iyarsa ta kinshin kasa wato PF.

Simbabwe, Ehemalige Präsident Kenneth Kaunda von Sambia
Tsohon shugaban Zambiya Kenneth KaundaHoto: AP

A fannin tattalin arziki kuwa, Zambiya ta sha samun bunkasa sai dai hakan bai taimaka ba wajen rage talauci a kasar. Kimanin kashi 70 cikin dari na 'yan Zambiya dai na rayuwa ne cikin talauci, yayin da manyan kamfanonin ketare suka fi cin gajiyar dimbin arzikin ma'adinai da kasar take da shi.

Die Bevölkerung Nordrhodesiens feiert nach der Wahl Kenneth Kaundas
A baya jam'iyya daya ce kawai ta mamaye fagen siyasar ZambiyaHoto: picture-alliance/dpa

Wani abu da ake nuna damuwa kai dangane da wannan kasa shi ne rashin mutunta hakkin dan Adam da mahukuntan kasar ke yi musamman ma a baya-bayan nan kamar yadda kungiyar Human Rights Watch ta nunar. Kasar dai ta yi shekara da shekaru ba tare da wani ci gaba a kokarin yi wa tsarin mulkin kasar gyara ba, yayin da ake yiwa 'yan adawa bita-da-kulli, da kuma matsin lamba kan masu neman jinsi guda yayin da kafofin yada labarai ke cigaba da kasancewa 'yan amshin Shata.