Shekaru 20 da kisan kare dangi a Ruwanda
April 10, 2014Talla
Shekaru 20 bayan kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Tutsi a kasar Ruwanda a shekara ta 1994, har kawo yanzu wadanda suka shaida wannan balahira na ci gaba da tuna dinbin tashin hankalin da suka gani a wannan lokaci. Mutane kamar su François Kabagema da a yanzu haka yake da kimanin shekaru 45 a duniya ya bayyana yadda ya shaidawa idanunsa yadda aka rika kashe mutane a yayin da yake ofishin jakadancin kasar Faransa a birinin Kigali na kasar Ruwandan. Zaku iya samun karin bayani a jerin rahotanni da ke cikin wannan kundi, kan wannan hali da al'ummar kasar ta tsinci kanta, da ma irin yadda dangantaka ta yi tsami da kasashen da Ruwandan ta yi zargi da hannu a kisan kare dangin.