1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar Pistorius ta dauki hankalin jaridu a Jamus

Umaru AliyuSeptember 13, 2014

Jaridun na Jamus a wannan mako sun yi sharhuna masu yawa kan nahiyar Afirka ciki har da ci gaba da samun cutar Ebola a Afirka Ta Yamma da Aiyukan kungiyar Boko Haram

https://p.dw.com/p/1DBoi
Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv
Hoto: picture alliance/AP Photo

Jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhinta, ta kwatanta Boko Haram ne a matsayin kungiyar ISIS ta Afirka. Tace ana ji ana gani, kungiyar tana ci gaba da kama garuruwa da yankuna a arewacin Najeriya. Yanzu ma dai Boko Haram tace tayi wa garin Maiduguri kawanya, a burinta na karbe jihar Borno baki daya. Shin samun nasarar hakan, zai kai ga rushewar Najeriya ne baki daya. Jaridar Süddeutsche Zeitung tace akwai alamun hakan, domin kuwa tuni shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau ya kafa abin da ya kira Khalifar Musulunci a yankunan dake hannunsa. Al'ummar farar hula sune suka fi shiga halin kaka-ni-kayi game da wannan al'amari gaba daya. Bayan dubbai da suka mutu, ko dai daga aiyukan yan Boko Haram ko daga hannun sojojin gwamnati, wasu dubbai sun zama yan gudun hijira a cikin gida, wasu kuma sun kaurace zuwa kasashe makwabta kamar Jamhuriyar Nijar.

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi nata sharhin ne kan cutar Ebola dake ci gaba da yaduwa a Afirka Ta Yamma, inda tayi misali da Liberiya. Jaridar ta tabo jawabin da ministan tsaron kasar Brownie Samukai yayi a gaban Majalisar Dinkin Duniya, inda yace Liberiya yanzu dai kadan ya rage ta rushe gaba daya, saboda cutar ta Ebola, wadda ta dakatar da rayuwa gaba daya a wannan kasa. Ministan yace asibitoci a Monrovia da sauran yankunan kasar sun cika, ba masaka tsinke, yayin da ake fama da karancin magunguna da ma'aikatan jiyya da likitocin dake da horo kan yaki da cutar ta Ebola. Wakiliyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan Liberiya, Karin Landgren ta kwatanta Ebola a matsayin wata sabuwar annoba da Liberiya bata taba ganin irinta ba, tun da kasar ta kawo karshen yakin basasa a shekara ta 2003. A daya hannun kuma, Kungiyar Hade Kan Afirka tayi kira ga wakilanta su dage takunkumin da suka sanya na hana al'ummar da suka fito daga kasashen dake fama da cutar Ebola shiga kasashen da cutar bata kai garesu ba tukuna. Tun da farko sai da ministan harkokin wajen Liberiya, yace ana nunawa kasarsa da sauran kasashen da cutar ta addaba kyama a Afirka.

Sharia'ar da aka yiwa sanannen magujin nan na nakasassu, dan Afirka Ta Kudu, Oscar Pistorius saboda zargin ya kashe budurwarsa a Johannesburg, ya dauki hankalin jaridar Tagesspiegel, wadda tace irin hukuncin da alkali Thokozile Masipa ta yanke bayan shari'a, ya zama babban abin mamaki. A hukuncinta, Alkali Masipa tace Pistorius ba ya kashe budurwar tasa da gangar bane, amma ya yi hakan ne cikin hali na rashin sani. Bayan sauraron shaidu na tsawon kwanaki 42, alkalin tace za a yankewa Pistorius hukuncin da ya dace da wannan kuskure da yayi nan da makonni biyu zua hudu. Ranar 14 ga watan Fabrairu na shekara ta 2013 ne Pistorius ya harbe budurwar tasa, Reeva Steenkamp a gidansa dake kusa da Johannesburg. Babban lauyan gwamnati yace Pistorius ya aikata hakan da gangar, tare da niyyar kashe ta, amma lauyoyinsa suka ce magujin yayi zaton dan fashi ne ya shiga gidansa, saboda haka ya kare kansa ta hanya amfani da bindigarsa.

Oscar Pistorius Urteil 12.09.2014
Oscar PistoriusHoto: Reuters/Siphiwe Sibeko

Jaridar Kölner Stadt Anzeiger ta rawaito game da wasu mutane biyar yan kungiyar nan ta Al Shabaab da aka kama a tashar jiragen saman Frankfurt da kuma can a Nairobi kasar Kenya. Jaridar tace mutanen guda biyar dukansu yan kungiyar ta Al Shabaab ne da tuni dama ake nemansu. A bisa rahoton gidan television na Jamus, wato ARD,matasan biyar Jamusawa ne da aka haife su, kuma suka taso a Bonn, kafin daga baya su karbi addinin musulunci. Jaridar tace gaba daya sai da suka sami horo a sansanonin al Shaabab, kafin a tura su su shiga kai hare-hare da kungiyar ta basu umurni.