1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Faduwar jirgin saman Germanwings

Alexander Kudascheff/ Mohammad Nasiru AwalMarch 27, 2015

Har yanzu ana cikin kaduwa da alhini tare kuma da yi wa juna jaje, inji Alexander Kudascheff babban editan tashar DW a cikin wannan sharhi da ya rubuta.

https://p.dw.com/p/1EygQ
Frankreich Absturz Germanwings A320 (Bildergalerie)
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Hitij

Har yanzu ana lalabe cikin duhu don sanin dalilin da ya sa mataimakin matukin jirgin saman Germanwings ya haddasa faduwar jirgin da gangan.

Ana iya cewa wani mafarkin abin tsoro ne na dan Adam. Wani mataimakin matukin jirgin sama ya nemi kashe kansa, da kawo yanzu ba a san manufarsa ba, amma ya yi setin jirgin samansa da gangan ya fadi ya hallaka kansa da sauran mutane 149 da ke cikin jirgin. Kashe kan ya zama wani kisan rayuka barkatai na fasinjoji da ba su san hawa ba su san sauka ba. Wannan dai wani cin zarafin irin yarda da kuma amincewar da fasinjojin jiragen sama a duniya baki daya suka yi wa matuka jiragen ne. Wannan lamarin dai shi ne guda daya tilo amma abin damuwa ne.

Tabbas yanzu ana bincike nan da can na neman dalilin da ya sa mataimakin matukin jirgin saman ya yi wannan aika-aika. Shin wa ke da hannu ko ma laifi? Wai shin da ba kamata ya yi a ce an gano irin matsalolin da wannan matashin ke da su a lokacin da ake ba shi horo ba? Shin ba a bukatar masana halayyar dan Adam a wajen horon? Watakila hakan na da kyau kuma yana da sauki. Domin sau da yawa masana halayyar dan Adam din suna gazawa musamman ma a takaddama tsakanin iyali. A lokuta da yawa kuma masana halayyar dan Adam din ba sa iya gane ainihin halin wanda ke zaune gabansu suna yi masa bincike. Amma yanzu ana son su dauki wani nauyi a cikin manhajar horas da matuka jirgin sama don a kwantar da hankali jama'a. Ko kadan wannan ba masalaha ba ce. Bugu da kari kwalejin horas da matuka jirgin sama na kamfanin Lufthansa ya shahara a duniya baki daya saboda ingancinsa.

Alexander Kudascheff DW Chefredakteur Kommentar Bild
Alexander Kudascheff babban editan tashar DWHoto: DW/M. Müller

Haddasa faduwar jirgin saman Germanwings da gangan abu ne da ya kada mu ya kuma jefa mu cikin halin tsaka mai wuya. Mun kadu mun kuma ji wannan fargaba a jika. Muna kokarin gane abin da ya faru. Muna neman wani bayani mai gamsarwa da zai saukaka mana fahimtar wannan ta'adi da ya auku a yankin tsaunuka na Alps da ke kasar Faransa. Sai dai abin ya wuce dukkan tunanin dan Adam.

Ana yi wa 'yan uwa wadanda abin ya rutsa da su jaje. Kuma kawo yanzu kafofin yada labaru sun nuna halin ya kamata dangane da mawuyacin halin da iyalan mutanen da abin ya rutsa da su ke ciki. Kamfanin Lufthansa ya nuna kaduwarsa ya kuma dauki alkawarin ba wa iyalan dukkan taimakon da ya dace. Su ma shugabannin siyasa sun nuna alhininsu. Ziyarar da shugaban Faransa Francois Hollande da Firaministan Spaniya Mariano Rajoy da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka kai wurin da jirgin ya fado ya tabbatar haka.

Su ma ma'aikatan ceto na Faransa da ke aiki ba dare ba rana sun yi rawar gani, wanda kuma ke nuni da irin zumunci tsakanin Jamus da Faransa. Karo na biyu ke nan a cikin 'yan watanni. A cikin watan Janeru ma an ga irin wannan zumunci bayan harin da aka kan ma'aikatan gidan buga mujallar Charlie Hebdo da kantin Yahudawa a Paris.

Shugabar gwamnatin Jamus wadda aka santa da kawaici, amma a wannan karon ta nuna kaduwarta a fili da aukuwar hadarin. Jamus dai na cikin kaduwa tana kuma cikin makoki.