1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanin makamar Siyasa da Shigarta

February 13, 2009
https://p.dw.com/p/DrHb
Hoto: gettyimages

Sanin makamar Siyasa da Shigarta.

Ga sabbin shiga harkokin Siyasa, akwai abubuwa na sarƙaƙiya da za a lura da su, shirin Ji Ka Ƙaru zai duba ya kuma nuna yadda Siyasa ke tasiri musamman ga masu yaƙin ‘yancin ɗan Adam.

Za a nuna yadda ‘yan siyasa ke tafiyar da harkokinsu a kuma nuna yadda Jama’a za su tinkari Siyasa, a kuma dama da su.

Yadda Ilimi ke Canja Rayuwa.

A wani shirin wasan kwaikwayo a rediyo za a duba yadda ‘yan siyasa ke holewa wanda ya canja rayuwarsu a yau. Wannan zai nuna wa jama’a yadda za a riƙa damawa da su. Shirin Ji Ka Ƙaru zai zama taɓa kiɗi taɓa karatu.

An yi shirin na Ji ka ƙaru a harsuna shidda, waɗanda suka haɗa da Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portuguese, da Amharic.

Shirin Ji Ka Ƙaru na samun gudunmuwa ne daga ofishin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Jamus.